Monday 2 October 2017

Magana Jari ce: MARA GASKIYA KO CIKIN RUWA YA YI JIBI

Tura Wannan Zuwa

Daga littafin Magana Jari Ce 2
Na Alhaji Abubakar Imam
(c) NNPC Nigeria

Wata rana wadansu Filani su bakwai suka tashi
daga rugarsu za su yawon sharo. Suna cikin
tafiya sai suka kai wani gari, suka ga in sun
wuce dare zai yi musu ba su kai gari na gaba ba.
Saboda haka suka sami wani katon zaure a gidan
Sarkin Fawa, suka sauka. Ashe guda na da kudi,
bai gaya wa kowa ba cikin ‘yan’uwan nan.
Sai can da dare suna hira, ya dauki kudin nan ya
kidaya su sule goma sha biyar, ya mayar ya kulle
a warki, ya ce, “Na she im mun je ni sai na samo
aure.”
‘Yan’uwansa suka ce, “Mun she mu ma ko da ba
mujo da kudi ba, da danshe na she ma samo.”
Can da dare ashe guda duk haushi ya kama shi,
don shi ba shi baya da ko anini. Sai ya tashi ya
sace kudin nan, ya kai ya binne, ya komo ya
kwanta.
Da gari ya waye za su tashi, mai kudin nan ya
kwance warki wai ya dauko kudi ya kidaya, kudi
suka ce dauke mu inda ka, ajiye. Ya fa tashi da
zage-zage, ya ce ‘yan uwansa suka sace don
bakinciki.
Da Sarkin Fawa ya ji zage-zage a zaure, ya fito
ya tambaye su. Mai kudin nan ya mai da jawabi
duka. Da Sarkin Fawa ya ji haka, ya yi kokari ya
sami wanda ya dauka, ya rasa. Sai ya ce wa mai
kudin, “Ka yarda, ko kuwa in kai ku ga Alkali?”
Mai kudi ya ce, “A’a? Sai a kai mu ga Alkali, na
she kudin nagge guda in yad da shi, ai ba shi
yiwuwa.
Sarkin Fawa ya sa su gaba har Majalisar Alkali.
Alkali ya tambayi mai kudin nan, ya bayyana
masa yadda aka yi. Da Alkali ya ji haka sai ya ce
wa sauran Filani, “Ashe da ma abin ba sacewa
kuka yi ba? Don Allah ku ba shi kudinsa, ku tafi
abinku. Da ya ke da wasa kuka dauka ai ba ku
bari a zo gaban magabata ba.”
Sai duk baki daya suka ce, “Renki shi dade, ai
mu ba mu daukar masa kudi ba.”

Alkali ya ce, “Haba, ku kun faye son wasa, na ce
ko kun gwada shi ne ku gani ko ya karaya. To,
ya yi raki, ku ba shi abinsa, ku tafi ku ba ni wuri.”
Filani suka tsaya tsakani da Allah su ba su
daukar masa kudi ba. Da Alkali dai yayi
wadannan ‘yan dabarunsa na mahukunta ya ga
abin ya ki, sai ya samo dogwayen sanduna guda
shida, ya auna tsawonsu, kowa na kallo, ya
yanke su dai dai da juna. Ya dauka ya rarraba
musu, ya ce wa Sarkin Dogarai, “Tafi da su gidan
wakafi sai gobe. An ce in wasa ku ke yi, ku fadi
gaskiya ku tafi, kun ki. To, in ni Alkali ne ba karya
ba, na kuwa gaji abin nan, kaka da kakanni, gobe
in kun zo a ga sandan barawon nan ta fi ta saura
da rabin taka. Ku jama’a, duk kun ga tsawon su
daya ko?”
Mutane suka ce, “I, Allah ya gafarta malam.”
Ya dubi Filani, ya ce, “Ku kuma kun gani hakanan
ne ko?”
Filanin suka ce, “I, Allah shi dade da renki.”
Alkali ya ce, “To, Sarkin Dogarai, tafi da su. Kai
kuwa Sarkin Fawa tafi da wannan mai kudin
gidanka sai gobe.” Suka tafi. Da dare ya yi tsaka,
kowa ya yi barci, sai barawon nan ya rasa abin
da ke masa dadi a duniya, ya tabbata gobe Alkali
daure shi zai yi in an sami sandansa ya karu da
rabin taka. Saboda haka sai ya gwada rabin taka,
ya zaro wukar da ke gindinsa ya yanke, ya ce
watau gobe in sandansa ya karu da rabin taka,
sai ya yi daidai da na saura.
Da gari ya waye Alkali ya zo gidan shari’a, sai ya
aika Sarkin Fawa ya zo, da bakonsa. Sarkin
Dogarai kuma ya taso keyar wadancan, kowa da
dogon sandansa a hannu. Da suka taru Alkali ya
ce, “To, jama’a, kowa ya matso ya gani.” Da suka
matso duk Filani suka zaro ido su ga ikon Allah.
Sai ya karbi sandunan ya gwada su, sai ga
sandan barawon ya kasa na saura da rabin taka.
Alkali ya fashe da dariya ya sa dogarawa su
tambaye shi sai ya nuna inda ya boye su.
Da Bafillacen nan ya ji abin ba dama sai ya ce,
“Wayyo Allah, she ma Alkali ya sa a bi ni in
kawo.”
Alkali ya cewa dogarai su kyale shi. Ya sa Sarkin
Dogarai ya bi shi inda ya binne, ya tono ya kawo.
Aka ba mai kudi abinsa.

Alkali ya sa aka yi wa barawon nan bulala shida,
aka daure shi wata uku. Saura kuwa ya sallame
su, suka koma rugarsu suka ba da labari. Da aka
sake shi sai ‘yan’uwansa suka yi ta yi masa ba’a,
suna kiransa “Dogo mai gajeren sanda.”

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

.
.
Source By ©Bukar Mada

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: