Monday 2 October 2017

Kissa Mai Kwadaitarwa Game Da Taimakon Bayin Allah Don Allah Da Kyakkyawar Manufa

Tura Wannan Zuwa Ga

Wata rana Umar Bn Ubaidullah ya fito zuwa
lambunsa,a lokacin da ya zo kusa da kofar shiga
lambun, sai ya ga wani yaro a zaune a gefen
lambun yana cin abinci, yaron yana cikin cin
abincin sai wani kare ya zo ya rika matsowa
kusa da da shi, sai yaron ya dauko loma daya ya
ba karen, sannan shi ma ya ci loma daya, haka
yaron ya rika cin loma daya yana baiwa kare
loma daya, sai Umar ya tsaya yana kallo yana
mamaki.
Sai Umar ya tambaye shi: "WANNAN KARENKA
NE?".
Sai yaron ya ce: "A'A".

Sai Umar ya ce: "To me ya sa na ga ka ba shi
rabin abincinka?".
Sai yaron ya ce: "Idan wani ya gan ni ina cin
abinci, to ai dole inyi masa Bisimillah".
Sai Umar ya yi mamakin yaron, sai ya tambayi
yaron: "Kai ďa ne ko bawa?".
Sai yaron ya ce: "Ni ďa ne daga cikin bayin da
suke aiki a wannan lambun".
Sai Umar ya tafiyarsa, can sai ya dawo ya yi wa
yaron busharar ya 'yanta shi, kuma ya ba shi
wannan lambun cikin farin ciki da yarda da shi.
Sai yaron ya ce: "TO KA ZAMA SHAIDA CEWA,
NA BAIWA TALAKAWAN MADINA KYAUTAR
KAYAN MARMARIN DA SUKE CIKIN LAMBUN".
Sai Umar ya yi mamaki, sannan ya ce masa:
"YANZU KA YI WANNAN KYAUTA DUK DA
TALAUCIN DA KAKE CIKI, DA BUKATUWAR DA
KAKE CIKI?".

Sai yaron ya ce: "INA JIN KUNYAR ALLAH
(S.W.T) YA BAN WANI ABU, KUMA IN ZO IN YI
MASA ROWA".

Ya tabbata a hadisi ingantacce cewa, Manzon
Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) ya ce: "Babu
wata rana da za ta bullo, face sai Allah (S.W.T)
ya wakilta wasu Mala'iku guda biyu, daya daga
cikinsu yana addu'a yana cewa, YA ALLAH KA
MAYARWA DA MAI KYAUTA ABIN DA YA BAYAR,
na biyu kuma yana cewa, YA ALLAH KA
TOZARTAR DA DUKIYAR MAI ROWA".

YA ALLAH (S.W.T) KA BA MU DAMAR YIN
KYAUTA DON ALLAH CIKIN FARIN CIKI DA
ANNASHUWA.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Halima S. Muhammad

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: