Friday 6 October 2017

KARANTA YANZU KA JI: YI TUNANI DA KYAU ANYA ZAMU TSIRA A YADDA MUKE A YANZU

Tura Wannan Zuwa
1. Naira 200 tayi girma da yawa
wajen bada sadaka a masallaci
amma tayi kadan kwarai a
lokacin biki ko wani hidima!


2. Minti 60 na zikiri a masallaci
yayi yawa sosai, amma minti 90
yayi kadan kwarai a wajen kallon
kwallo

3. Awa 1 ko 2 a masallaci don
daukar karatu yayi yawa, amma
mukan bata awanni wajen kallon
fina finai!

4. Bada lokacin karanta aya 20 na
Al-qur'ni yayi kunci, amma
mukan shafe kimanin awa 3 ko 4
muna karanta shafukan yanar
gizo ko jaridu cikin farin ciki!

5. Imani da gaskata labarin
jaridu, amma sai kwane-kwane
da shakka da tsabar tuhumar Al-qur'ani da hadisin
Manzon Allah (s.a.w) musamman
in sukaci karo da son zuciyar mu!

6. Karanta labarun dariya a
facebook ko whatsapp, amma
mukan kasa karanta ko layi 1 na
posting akan abin da ya shafi
addinin musulunci!

7. Muna saka TV a gaba na
tsawon awanni amma muke
kasa minti 15 muna ganin gabas
domin ibada!

8. Haddar wakoki basa bamu
wahala, amma mukan ga
wahalar haddar Ayoyin Al-qur'an
mai girma.

YA JAMA'A MUYI TUNANI!!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin, Sharhi ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user