Friday 6 October 2017

Labari: KO KA TABA JIN WANNAN LABARIN???

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani mutum ne ya shirya yin
tafiya tare da matarsa da
'ya'yansa a cikin motarsa suka
kama hanya. Ba su yi nisa ba
suka hadu da wani mutum a
tsaye a bakin hanya. Nan da nan
ya fara daga musu hannu, suka
tsaya, ya nemi su dauke shi su
rage masa hanya. Maigida ya
tambaye shi: "wane ne kai?"yace,
"ni ne dukiya." nan take matar da
"ya'yan suka yi tsalle suka ce lallai
a dauke shi su tafi tare Dama
motar irin babbar jif din nan ce
mai yalwar kujerun zama, suka
dauke shi suka kama hanya. Suna
yin gaba kadan sai suka tarar da
wani mutumin, shima a bakin
hanya yana daga musu hannu.


Maigida ya sake tsayawa, ya
tambaye shi: "wane ne kai?" yace
da shi:"ni ne sarauta da
matsayi."iyalannasa na jin haka
suka sake cewa a dauke shi,
domin babu wani abin da zai
gagari mutum a nan suka dauke
shi suka wuce tare da shi. Suna
kara yin gaba kadan sai ga wani
mutumin shima a tsaye a gefen
hanya, ya daga musu hannu suka
tsaya. Maigida ya tambaye
shi:"wane ne kai?" yace:"ni ne
addini."maigid ya waiwaya ya
kalli iyalansa. Sai yaga sun yi
jugun-jugun sun bata rai. Tun
kafin ya nemi shawararsu suka
ce:"wannan ba abokin tafiya
bane. Takura mana kawai zai yi
hukunce-hukuncensa na halal da
haram. Ya hana mu mu sakata
mu wala. Ya dai jira nan gab
kadan mun dawo mu dauke shi
bayan mun gama cin karanmu ba
babbaka."maigida ya ce babu
shakka kun fadi gaskiya,kuma
wannan shawarar taku abr
dubawa ce, suka wuce suka bar
addini nan tsaye suna masu
alfahari da wadatar dukiya da
alfarmar sarauta da matsayi har
suka ci karfin tafiya da zasu yi.


Suna kan wannan tafiya, suka isa
wani wurin binciken abubuwan
hawa. (cheking point) suka tsaya
don suna a duba su. Sojan da ke
bincike yace da maigida:"kai fito
mu tafi, tafiyarku ta kare daga
nan!" maigida yace:"kai kuwa
wane ne kai?" yace: "ni ne
mala'ikan mutuwa. Ina bincike
ne a kan addini. Kai kuwa baka
tare dashi." maigida yace. Af, ai
na baro shi a hanya, Bari na
koma na dauko shi, mala'ikan
mutuwa yace: ai wannan damar
ta riga ta wuce ka har abala! Mai
gida ya kara cewa, to ai ina tare
da dukiya da sarauta da matsayi
da kuma dukkanin iyalina,
mala'ikan ya sake cewa dashi.


Ai dukkani wadannan baza su
amfanar da kai komai ba, addini
ne kadai ake da bukata a nan,
maigida ya wai yaga matarsa tayi
sauri ta dare kan kujerar
direba.taja mota a guje suka yi
tafiyarsu, ita da sauran 'ya'yansa
da dukiya da sarauta da matsayi.

Nan suka bar shi mala'ikan
mutuwa ya tasa keyarsa babu
iyali! Babu dukiya!! Babu sarauta
da matsayi!!! Don Allah dan 'uwa
wane darasi ka dauka dangane
da wannan labarin? 


INA FATAN
ZA KA ILHAMANTU DA WANNAN
LABARIN KASAN CEWA DUNIYA
BATA JIRAN KOWA. ALLAH YASA
MUDACE.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: