Friday 6 October 2017

Rayuwar Facebook Hahaha Hattara Samari da 'Yan Mata

Tura Wannan Zuwa Ga

Watarana wani bazazzage yana
zaune sai mahaifinsa ya kirashi
yace dashi "Kai Ilu ! Zo ka duba
mini facebook din wayata bata
yi, bansan menene suke bukata
yau kuma ba''

Ilu ya taso ya karbi wayar ya
duba sai yaga ashe babu Data
ne (wato MB) a layin. Sai Ilu
yace ai baubu MB ne a layinka
shine yasa, yanzu sai ka saya
MB ko kuma kayi subscribtion.

Koda fadin haka sai uban ya
kama surutu yana cewa "Nifa na
gaji da yawan kashe kudin nan,
gwara ma kawai na daina
facebook din, domin tunda
kanenka ya bude mini facebook
nan kullum sai sun nemi, yace
mini kudin FACEBOOK SIGN UP
naira dubu biyar na biya, ya
sake cewa dole sai an biya
kudin CHATING PERMIT dubu
uku shima na bashi ya kai,
makon da ya gabata yace wai
sunce in biya kudin PROFILE
PICTURE dubu hudu shima na
bashi ya kai musu, daga baya
sunce yazo ya karbi kudin
FRIEND REQUEST dubu uku a
haka nace ya basu hakuri sai na
dawo kasuwa, bayan na dawo
kuma na bashi kudin ya kai.

Shekaran jiya sunce yazo ya
karbi kudin NOTIFICATION dubu
daya, bani da ko sisi amma sai
da naje na karbi bashi nazo na
bashi yakai musu, jiya ma yazo
ya karbi kudin shiga GROUP
dubu biyu, kudin
INTERNATIONAL FACEBOOK

PASSPORT dubu shida, dazun
da safe kuma ya karbi kudin
UPDATING dubu uku yakai
musu, kafin nan ya dawo na
kiraka ka duba mini kai kuma
kace sunce akai kudin wani abu
wai shi MB ! YANZU DAMAN
KUMA HAKA KUKE KASHE KUDI
KULLUM A FACEBOOK DIN
AMMA BAKU FITA DAGA
KUNGIYAR FACEBOOK DIN
BA ????
,
,
IDAN KAINE ZAKA FADA MASA
GASKIYA NE KO ZAKAYI
SHIRU ???

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Khaleepher Abubakar

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: