Friday 6 October 2017

Labari: An sami labarin barkewar annobar cutar kyandar Biri a jihar Bayelsa da ke yankin Niger Delta a tarayyar Najeriya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta tabbatar da afkuwar
barkewar annobar cutar Biri a jihar Bayelsa,
kuma ta ce an kebe kimanin mutane goma da
suka kamu da cutar kana ana ci gaba da neman
wasu da dama da ake kyautata aton sun kamu da
wannan cuta domin a killace su wuri daya.

Hukumar kula da lafiya ta jihar ta aika da
amfarin kwayar cutar ga sashin bincike da gwaje
gwaje na hukumar lafiya ta duniya dake kasar
Senegal domin tantancewa yayin da sakamakon
gwajin zai tabbatar ko annoba ce.

Rahotanni sun bayyana cewa daya daga cikin
mutane goma da suka kamu da cutar likita ne,
kuma yanzu haka ana neman mutane arba’in da
tara domin a kebe su, wasu rahotanni kuma sun
bayyana cewa akalla mutane goma sun riga
mugidan gaskiya a sakamakon kamuwa da cutar.

Mr Daniel Maxing, shine kwamishinan ma’aikatar
watsa labaru a jihar ta Bayelsa, ya sami zantawa
da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka,
Abubakar Lamido Sakkwato, ta wayar salula
kuma ya bayyana masa cewar akalla mutane
goma na kebe a yanzu haka domin kaucewa
yaduwar cutar.

Jama’a da dama a fadin jihar sun bayyana halin
da ake ciki a matsayin masifar data shafi kowa
da kuma yin kira ga gwamnati data gaggauta
shawo kan lamarin. A halin da ake ciki dai jama’a
da dama basa musabaha da juna kamar yadda
aka saba domin gujewa kamuwa da wannan cuta.

Cutar kyandar Biri dai ta samo asali ne daga
Birai da kuma sauran dabbobi da ake mu’amulla
da su irin su barewa.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: