Wednesday 4 October 2017

LABARIN WASU SAMARI MAI HAKURI YA KAN DAFA DUTSE

Tura Wannan Zuwa Ga

A kasar Sin, anyi wadan su abokai guda biyu,
dukkan su sun kasance suna da kusumbi a baya.


Daya sunan shi Cheng dayan kuma sunan shi
Zing.


Cheng ya kasance mutum ne mai saukin kai
kuma mai godiya ga Allah a duk halin da ya sami
kan sa a ciki. Amma Zing mutum ne wanda
halayen sa idan aka zuba a tire to ko kare baya
ci.


Kullum tunanin Zing bai wuce na yadda zai yi ya
rabu da kusumbin nan na shi ba, yayi biyar
bokaye da yan bori da yan tsibbu amma duk a
banza, kusumbi kullum kamar ana kara masa
girma. Cheng yayi bashi shawara akan ya dogara
ga Allah kan lalurar da ya dora masu amma Zing
yaki sauraren shi.

Wata rana Cheng ya fita shan iska bayan gari, da
goshin magariba, sai ya ratse gun wata itaciyar
tsamiya ya tsuguna domin yayi fitsari. Ashe
kuma akwai wasu yaran aljanu sun fito neman
kwallon su da ta bata. Suna ganin Cheng sai
daya daga cikin su yace, "Ai kuwa ga kwallon mu
can a bayan mutumin nan mai fitsari".


Cheng na tsugune bai san abun da ke faruwa ba,
sai yaji anyi wuf ancire mashi kusumbi. Ya tashi
da gudu sai gida. Daga ranar Cheng ya rabu da
kusumbin sa, ya koma lafiya lau.
Da Zing yaji labarin yadda Cheng ya rabu da
kusumbin sa, sai shima ya shirya goshin
magariba ya nufi bishiyar tsamiyar nan. Yana
zuwa sai ya tsuguna kamar yana fitsari. To ashe
kuma rannan bayan aljannun nan sun cire
kusumbin Cheng sun gane kwallon su.

Suna ganin Zing a tsugune wurin sai suka ce
Allah sarki ga mutumin nan can da muka dauke
kwallon sa ya dawo nema. Kuyi sauri ku mayar
masa da kwallon shi tunda mun gane tamu.


Zing na tsugune yana jira yaji an cire mashi
kusumbi, sai yaji wuf an dambara mashi wani
kusumbi a baya. Zing ya tashi kusumbi gaba
kusumbi baya.


Don haka ko da yaushe mu kasance masu godiya
ga Allah a duk halin da muka tsinci kan mu a
ciki. Hausawa ma sunce ka gode ma Allah ko a
bakin kura kake.



Source By ©Waziri Aku

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user