Wednesday 4 October 2017

SHIN KO KASAN LOKACI BAYA JIRA KARANTA WANNAN???

Tura Wannan Zuwa Ga

Audu da Musa sun kasance abokan juna ne, tun
suna yara tare su ke wasa, tare su ke zuwa
makaranta a takaice bacci kadai ke raba su.

Audu ya kasance yaro ne mai yawan son
wasanni da kuma kallace-kallacen kwallo da
sauran fina finai. Musa kuwa yaro ne mai kakarin
neman ilimin addini, a duk lokacin da Audu ya tafi
wurin wasan kwallo, shi kuma Musa yakan tafi
makarantar islamiya ne.

Musa ya yi iyakar kokarin sa ya jawo hankali
Audu domin ya lura da duniya, ya dinga kulawa
da addinin sa, amma ina shaidan ya riga ya yi wa
Audu huduba da ya ci gaba da more rayuwar sa,
duka duka shekarar ka nawa? Ba ka wuce
shekara ashirin ba, ka ga kana da sauran lokaci,
ka more rayuwar ka, daga baya sai ka tuba...

akwai lokaci! Wannan dai ita ce hudubar da
shaidan ya ke yi wa Audu a kowane lokaci.
Wata rana tafiya ta kama Audu da Musa zuwa
wani gari. Bayan sun shiga mota an fara tafiya
sosai, sai tayar motar ta fashe, motar taje ta
bugi bishiya ta bangaren da Audu yake zaune.
Aka kawo musu gudummuwa aka ciro dukkan
mutanen da suke cikin motar. Allah ya tsare
Musa bai ji ciwo ba.

Amma Audu da yake ta bangaren sa ne motar ta
bugi bishiya, koda aka ciro shi baki da hancin sa
duk jini ne yake fita, yana magana da kyar yana
cewa, "Ina Musa? Don Allah a kaini asibiti, bani
son na mutu yanzu, don Allah a kawo man ruwa
na yi sallah, idan na mutu yanzu bansan abun da
zan tarar ba" Amma ina, Audu bai san lokacin sa
ne ya yi ba. Kafin a kai shi asibiti ya ce ga garin
ku nan.

To kunga karshen Audu, shaidan ya hure masa
kunne ya hana shi ya tuba amma bai fada masa
lokacin da zai mutu ba.

Don haka muji tsoron
Allah mu tuba tun lokacin mu bai kure ba. Babu
wanda yasan ranar da zai mutu, kila mu mutu
nan da shekara biyar, kila shekara daya, kila
gobe kai kila ma saura yan sa'o'i kadan mu
mutu. To mai zai hana mu tuba da wuri.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Waziri Aku

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: