Monday 20 November 2017

Hausa Films: Masifar da take addabar Kannywood a halin yanzu-Adam A. Zango

Tura Wannan Zuwa

OPEN LETTER TO MY HATERS IN KANNYWOOD

Ni ba dan daudu bane kuma ni ba dan maula
bane. Sannan ni ba mushiriki bane, bani da
malami ko matsafi. Da ALLAH kadai na dogara.

Idan kuma akwai malamin da yace na taba zuwa
wajansa ko kuma wanda ya taba bani kudi
kyauta ba tare da nayi masa aikin komai ba, toh
dan girman ALLAH kada ya rufa min asiri tun
daga kan yan siyasa, sarakuna, gwamnati, ko
masu kudi, ko yammata…. duk abinda dana
mallaka a rayuwata gumi na ne ya bani ba dan
adam ba…motar hawa, gida ko fili….

Don haka
babu wanda ya isa ya sani inyi abinda banyi
niyya ba tunda babu wanda ya tayani kare
mutuncin daukakata.

DON HAKA TA HANYA DAYA KADAI ZAKU IYA
DAKATAR DA DAUKAKATA……

HANYAR ITACE
KU DAKATAR DA NUMFASHINA, SAI DAI KUMA
KASH HAKAN BA’A HANNUNKU YAKE…. HABA
KUYI TA YAWO DANI KUNA BATA MIN SUNA
DON KAWAI ALLAH YA FIFITANI AKANKU.

Kunce min arne kunce min gay kunce min fasiki
kunce min mai girman kai amma duk da haka
masoyana basu gujeni ba basu daina sayan fina
finai da wakokina ba.

Haba don ALLAH mai nayi muku duk wanda na
taimaka a rayuwata sai ya dawo yana yakata!!
Toh na kai bango…… billahillazi la’ila ha illahuwa
duk wanda ya kara kara tabani saina tona masa
asiri.

Sannan duk wanda ya rufa min asiri akan
abubuwan dana lissafa ALLAH ya tona masa
nasa.

Ban kira sunan kowa ba a yanzu amma
next time zan kira sunan ko waye idan ya kara
bata min suna ….ina da ýaýa ya zama dole in
fara kare mutuncina da martaba na kafin yayi
affecting dinsu don ALLAH kadai ya san gawar
fari…. sannan zanja tunga da mabiyana na
kannywood…. don a haka ne kadai za’a bam
bance tsakanin aya da tsakuwa….

MASOYANA KU GAFARCE AKAN ABUBUWAN
DANA RUBUTA, AN KURE NI NE”

YADDA AKO INA AKE SAMUN NAGARI DA BATA
GARI HAKA ZALIKA A CIKIN AKWAI NAGARI DA
BATA GARI KUMA

Wallahi billahi daga yau baza’a
kara yi min kazafi inyi shuru ba don kowa a cikin
ya san kowa.

Shiyasa idan akace mana jahilai
bana damuwa yanzu domin nima na gano hakan.

Tunda ance amfanin ilimi aiki dashi.
Masifar da masana’antar kannywood take ciki ya
wuce misali. Saboda zalinci, fasikanci, riya, eye
service da kuma cin amana da ake aikatawa
karara amma daga anyi magana sai muce matan
cikimmu ne suke janyo mana.

Wlh matammu
basu da laifi domin addini bai taba baiwa mace
damar zama babu mai kula da ita ba.

Amna a
kannywood film daya yarinya ko yaro zasuyi sai
kaga sun bude kamfanin kansu harma su rinka
daukar sababbin yan wasa.

Babu tone tone domin da dama sun san inda na
dosa.

DON HAKA MU DAINA JIN HAUSHIN ZAGIN DA
WASU AL’UMMA SUKE MANA!!

Mu karba
laifukammu mu gyara wata kila nan gaba kadan
suyi alfahari damu.

Duk abinda na rubuta idan akwai karya a ciki
wani ya fito ya karyata ni ko kuma a koreni.

DUK WADDA DA TACE SAINA NEMETA KAFIN IN
SAKATA A FILM TA FITO GIDAN TV KO REDIO
STATION TA FADAWA DUNIYA.

IDAN KUMA TA
RUFA MIN ASIRI ALLAH YA TONA MATA NATA
ASIRIN.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: