Monday 20 November 2017

Labari: Yadda Wata Mata Ta Hallaka Mijin ta Har Lahira yana Sallah-Maryam

Tura Wannan Zuwa Ga

A yayin da ake cigaba da juyayin rikicin
ma’auratan nan da ya jawo matar ta kashe
mijinta, wasu rahotanni sun bayyana cewa ashe
matar mamacin ta samu nasarar soka masa
wuka ne sa’ilin da ya kabbara Sallar isha’i

Majiyar Hausa Times ta ruwaito wani
Makusancin dangin marigayi Bilyaminu Bello, ya
shaida masu cewa a ranar Asabar da daddare,
rikici ya barke tsakanin Maryam da maigidan
nata bayan ta karanta wasu sakonnin tes a wayar
mijinta, wadan da suke dauke da kalaman
soyayya, abinda yake tabbatar mata da cewar,
yana soyayya da wata daban a waje.

Jaridar Daily Nigerian a hirar da tayi da wani
makusancin mamacin, yace, sun yi zaton sabanin
da aka samu tsakanin ma’auratan biyu ya wuce,
lokacin da Kawun Maryam din ya shiga cikin
al’amarin domin sasantawa.
Kamar yadda ya shaidawa majiyar tamu, Maryam
ta samo sharbebiyar wuka a dakin girki (kitchen),
sannan ta jira lokacin da mijin nata ya kabbara
Sallar Isha, sannan ta kaddamar masa da
mummunan hari, inda ta sassoka masa.

“A lokacin da ta soke shi a bayansa da kirjinsa
da kuma ‘ya ‘yan marenansa, nan take ya fadi
kasa yana marari tare dafatan ta taimake shi.

Maryam na kallonsa, kwance male-male cikin jini,
yana rokonta da ta taimaka masa don ceton
rayuwarsa.

“An jiyo shi yana cewar ‘Maryam ki taimake ni…

Maryam ki taimake ni, har ya kai gargarar
mutuwa yana kiran da ta agaje shi, amma shiru
tayi tsaye tana kallonsa, har ya kasa yin wani
katabus, sannan ta bara.

“Maryam kawai cewa take, Allah ne ya tona
maka asiri, tana maimaitawa, har ya rasu a
wajen.

“Awa daya bayan wannan dambarwa ta auku,
lokacin da taga baya ko motsi, sannan ta nemi
taimakon makota da su taimaka mata a sanya
shi a cikin mota domin ta kaishi asibiti.

“Asibitin farko da suka je, sun ki yadda su duba
shi sabida halin da suka ganshi suka ce sai da
dan sanda, sai da suka je wani asibitin ne,sannan
jami’an asibitin suka kirawo ‘yan sanda, kuma
Maryam ta tabbatar da cewar ita ce ta cakawa
mijin nata wuka har ya mutu” A cewar dangin
mamacin.

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: