Thursday 9 November 2017

RAYUWAR MATA A SOCIAL NETWORK

Tura Wannan Zuwa
Kamar yadda kowa ya sani, mata mutane ne
masu yanci, daraja, qima, girma, mutunci,
karamci, tare da girmamawa a cikin al'umma.




Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Zan iya cewa kusan kashi tamanin cikin dari na
wahalar da maza suke sha, domin su ne, in dan
ta namiji ne shi kadai, wani abinda zai samu a
rana daya, ya isheshi harqallar sati daya, kaga
kenan, sauran ranaku shidan ba sai ya fita nema
ba.

Mata sun kasu kaso shida a social network,
kowanne da dalilinsu.

1- Na farko sun zo social network ne domin su
sada zumunta ga yan uwansu, qawayensu na
makaranta, tare kuma da yin wasu sababbi daga
nan gida Najeriya da kuma kasashen ketare.

2- Kashi na biyu kuma sun zo ne domin kawai
sun ga qawayensu suna yi, ko kuma saboda jin
labarinsa da sukeyi a gari da kuma kafafen yada
labarai, wato dai suma suga me ake gani a ciki.

3- Kaso na uku kuwa sun zo ne neman saurayi
dan kwalisa, mai iya kalaman soyayya, mai abin
hannu (ga yammata kenan), ko kuma bazawari
(ga zawarawa su kuma).

4- Na hudu kuwa kawai sun zo ne domin neman
ilmin addini, ilmin sana'a, ko kuma ilmin boko
(domin kuwa babu kalar group din da babu).

5- Kaso na biyar kuwa, kawai gasu nan ne, babu
wata hujja na zuwan nasu ko kuma dalili, in tayi
dadi suyi dariya, idan kuma ta 6aci suyi Allah
wadarai.

6- Kaso na shida kuwa sune wadanda suka hada
biyu, ko uku, koma hudu daga cikin hujjojin da
aka lissafa a sama, (wato dai su hujjar zuwansu
tafi daya).

Amma duk da waɗannan hujjoji na zuwan matan
social network, wasu mazan basa duba haka,
burinsu kawai matan su tsaya su sauraresu, ko
da kuwa abinda suka zo dashi ba mai ma'ana
bane.

Nakan tausayawa mata idan na tuna tarin inbox
din da ake yi musu, ga tulin freind request,
notification ma ba'a barshi a baya ba, ga tagging
dinsu da akeyi walau a posting, hoto, ko kuma
timeline dinsu musamman idan mace ta saka
hoton ta, ko kuma ta fiya magana a social
network, gashi a ringa dibarsu ana zubawa a
group mai amfani da mara amfani.

Kowa kuma daga cikin masu yiwa matan haka,
babban burinsa ta saurareshi shi kadai, baya
tunanin sauran masu irin halayyarsa, idan kuwa
aka samu akasin haka, to ranar zata sha zagi da
tsinuwa.

Abin tambayar a nan shine, Wai shin ku masu irin
wannan halayyar an gaya muku saboda ku suka
zo social network?

Shin kun san da cewa akwai aljanun gaske a
cikinsu kuwa?

Ko kun san da cewa ba dukansu ne matan ba,
domin kuwa akwai maza da suke amfani da
sunan matan?

Ko kun san da cewa da yawa daga cikin matan
suna da samarin da suke so?

Wadannan tambayoyi da makamantansu suna  nan jibge amma fa sai anyi tunani.
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user