Thursday 4 January 2018

Karanta Kaji: Akwai rudani kan asibitin da aka kwantar da dan Shugaban kasa

Tura Wannan Zuwa

Hadarin da da Yusuf Buhari dan Shugaban kasa Buhari ya yi a babur ya haifar da rudani game da asibitin da aka kwantar da shi, domin a yayin da gwamnati ke cewa yana nan a wani asibiti da ke Abuja, wadansu kafofin yada labarai kuma na nuna cewa an tafi da shi kasar Jamus.

Hadarin ya haddasa ya samu karaya a hannu da kuma rauni a kansa, kwanaki biyu bayan faruwar lamarin, inda ya kasance karkashin kulawar wani asibiti da ke Abuja.

Al’amarin ya faru ne a daren Talatar da ta gabata, kamar yadda wata sanarwa daga fadar Shugaban kasa ta bayyana, mai dauke da sa hannun Mai Taimaka wa Shugaban kasa kan Harkokin Yada Labarai, Malam Garba Shehu.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa an fita da Yusuf din zuwa kasar Jamus ne a jirgin daukar majinyata tare da rakiyar wani kwararren likita da kuma wasu jami’an lafiya uku.

Sai dai da aka tuntubi fadar Shugaban kasa dangane da batun fitar da Yusuf zuwa Jamus, Garba Shehu ya musanta, cewa wannan ba gaskiya ne ba.

Tun da farko sanarwar ta bayyana cewa Yusuf din yana samun sauki kuma yana samun kulawar da ta kamata, inda sanarwar ta kara da cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mai dakinsa A’isha Buhari suna matukar godiya ga al’ummar Najeriya bisa addu’o’i da kuma fatan alheri ga dan nasu.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar da hadarin ya faru, Yusuf ya halarci bikin murnar cika shekara 50 na Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara a babban dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja tare da ’yar uwarsa Halima Buhari da mijinta, inda aka ruwaito cewa har karfe shida da rabi na yammacin ranar yana wurin.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: