Saturday 27 January 2018

KARANTA KAJI: Kai Dole Buhari ya mika mulki kamar yadda Jonathan yayi a 2015 – inji Sule Lamido

Tura Wannan Zuwa Ga

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa,Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewar a zaben 2019 da yake tafe, idan ‘yan Najeriya suka kayar da APC da Buhari tilas ne shima Buhari da APC su yarda da sakamakon zaben, kuma su karbi faduwa kamar yadda Goodluck Jonathan yayi a 2015.

Daily Nigerian ta ruwaito Sule Lamido ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a wani taron tattaunawa kan batun zaben 2019 da kalubalen da suke tattare da zabe.

Taron dai kamfanin Mediya Trust masu buga jaridar Daily Trust ne suka shirya shi a Abuja domin tattaunawa kan zaben 2019.

A yayin taron, Sule Lamido daga bangaren jam’iyyar PDP ya gabatar da dogon jawabi kan batun siyasar Najeriya da kuma irin abubuwan da jam’iyyar PDP tayi na bajinta game da zaben 2015 da ya gabata.

“Tilas ne a ramawa kura aniyarta a zaben 2019, idan PDP ta kayar da APC dole ne su karbi faduwa kamar yadda muka yi a baya”

Sai dai a nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha, ya mayarwa da Sule Lamido martani, yace indai Sule Lamido ne zai yiwa PDP takara to ba makawa Buhari yaci zabensa karo na biyu.

Haka nan, shima Sanata Saidu Dansadau ya kalubalanci kalaman na Sule Lamido, inda yace duk abinda Sule Lamidon ya fada game da PDP ba gaskiya bane.

“A babban taron PDP na shekarar 1998, ai Sule Lamido bai goyi bayan Obasanjo ba, ya goyi ayan Alex Ekwueme ne ya zama dan takarar PDP”

Tsohon Gwamnan jihar Legas, kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ne ya wakilci jam’iyyar APC a wajen wannan tattaunawa da aka yi domin duba yadda zaben 2019 zai kasance.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Hausa Times

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: