Saturday 24 February 2018

ME YASA IDAN TSUNTSAYE SUKA TABA WUTARLANTARKI BATA YI MUSU SHOKIN???

Tura Wannan Zuwa Ga
Sau da yawa mutane kan yi mamakin yadda
tsuntsaye ke gad'ar su a kan wayoyin
lantarki ba tare da ta wujujjugasu ba.

Shi ko d'an Adam, da zaran an samu
kuskure ya tab'a ta, sai ta ja shi tamkar
maganad'isu da ka iya hallaka shi.

D'an Adam tun yana yaron sa ake nuna
masa irin had'arin da wutar lantarki take da
shi, da kuma nisanta shi da yin wasa kusa
da ita. Haka kuma, ya san kauce wa sa y'ar
yatsar sa a ramin soket, da yin taka tsantsan
wurin amfani da kayan lantarki a kusa da
ruwa ko kuma idan sun jik'e, da kuma
k'auracewa duk inda wayoyin lantarki su ke,
musamman ma inda aka yi jone-jone da
kuma falwayoyi. Guje ma hakan, ka sa
mutum ya tsira daga hatsarin shokin, da ka
iya halakarwa nan take.

Ita dai wutar lantarki, na tafiya ne ta hanyar
tunkud'owar da sinadaren haske da ake kira
(electrons) ke yi ta kwandakta (conductor).
Wayar wuta ko tagulla ko jan karfe (copper),
ita ke ba wutar lantarki damar tafiya a
sauk'ake a kan ma'aunin ta.

Idan muka waiwaya baya domin amsa
tambayar mu ta faro. Shin ko wani dalili ya
sa tsuntsaye wuta bata jan su?

Dalili kuwa shi ne; su dai tsuntsaye ba su jin
shokin a yayin da suka sauka a kan wayoyin
lantarki, sabo da ba su da kwandakta mai
kyau da wutar lantarki ke so a yayin da take
tafiya a cikin wayoyi.

Bugu da k'ari,
kasancewar kwayoyin halittu wato (cells) da
na tsokoki (tissues) d'in tsuntsaye, ba su ba
wa sinadaren wutar lantarki (electrons)
damar wucewa a sauk'ak'e kamar yadda su
ke wucewa a kan jan k'arfe ko tagulla
(copper).

Wutar lantarki na tafiya ne da ga wuta mai
k'arfi zuwa mara k'arfi (high to low voltage).
Haka kuma tana zuwa ne a kan layi d'aya na
wuta da k'arfin ta ya kai dubu talatin da
biyar (35000 volts).

A yayin da take wucewa
da k'arfin ta, ko da tsuntsaye sun hau kan
wayar, sai dai ta wuce ba tare da sun san an
yi ba.
Duk da cewa masana sun ce ba k'arfin
wutar ke kisa ba. Amma da yake k'arfin
wutar ya bambanta kuma akwai adadin da
ake buk'ata domin samar da makamashin
wutar lantarki.

A yayin da tsuntsu ya sauka a kan layin
wutar da k'arfin ta ya kai dubu talatin da
biyar da aka fad'i a baya, to sai tak'i ma
tsuntsun komi sabo da ba a samu bambacin
k'arfi ba, (abun nufi shi ne, karfin wutar na
nan yadda ya ke bai canza ba).

Amma idan
da za a yi rashin sa'a, tsuntsun ya mik'a
fiffiken sa, zuwa wani layin wuta ta daban, to
fa da labari ya canza, domin fizgan shi za ta
yi, har ta kai shi lahira. K'aramin misali shi
ne; "jemage" shi idan ya tashi sauka kanta,
afka mata yake yi, duk sai ya tab'a biyun
gaba d'aya, shi yasa yake yawan mushe a
kan ta. Duba da irin haka ne, ya sa
kamfanonin dake samar da wutar lantarki ke
bada tazara tsakanin waya da waya a
falwayoyi.

Haka kuma, a kan binne wayoyin lantarki a
k'asa sosai, domin guje wa hatsarurrukan da
ke tattare da ita. Shi ya sa da zaran mutum
ya tab'a ta, sai ta jijjiga shi ko ta fisge shi,
sabo da jikin mutum na da alak'a da k'asa,
da kuma kwandakta mai kyau da wutar
lantarki ke so.

Dama ita wutar lantarki, sinadarin da ake
samu na karen (current) daga wuta mai
k'arfi ne zuwa mara k'arfi. Shi ya sa, za ta
so jikin d'an Adam, domin yana da alak'a da
ta k'asar da aka binne, shi zai k'ara bata
dama ta tafi yadda ya dace. Dalin haka ne
ya sa, da zaran mutum zai tab'a wutar
lantarki sai ka ga ya jawo takalmi ya sa,
domin gujewa ja idan babu takalmi a k'afar
sa.

To ko me yasa su ma'aikatan kamfanonin
wutar lantarki ba ta cika jan su ba?
Dalili kuwa shi ne; kayan aikin su na da
garkuwar da ke kare su daga hatsarin wutar.

Haka kuma, safar hannun da suke sawa, ta
roba ce da ke hana ko wace irin wuta mai
k'arfi da mara k'arfi samun damar tab'a
jukkunan su.

Source by  ©Farouk abdullahi Tukuntawa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user