Friday 2 February 2018

Za'a Sanya Dokar Hana Matasa Facebook Musamman Hausawa A Kiyaye Saboda Tsaro

Tura Wannan Zuwa Ga
Sama da kwararru 100 na lafiyar yara na bukatar hukumar shafin Facebook ta janye manhajar da ta kirkiro ta amfanin yara 'yan tsakanin shekara 13.

A wata budaddiyar wasika da suka aika wa shugaban Facebook Mark Zuckerberg, kwararrun sun kira manhajar mai suna ''Messenger Kids'' a matsayin wani yunkuri da bai dace ba na karfafa wa yara amfani da Facebook.

Masanan suka ce lokaci bai kai ba da yara za su mallaki shafukan sada zumunta da muhawara nasu.

Hukumar ta Facebook ta ce an tsara manhajar ne tare da shawarar kwararru kan kariya ga miyagun abubuwa, kamar yadda iyaye suka bukata kan yadda za su kasance da iko da kuma sanin abin da 'ya'yansu ke yi a shafukan sada zumunta da muhawara.

Manhajar samfurin Messenger ta Facebook an saukakata ba kamar ta manya ba, kuma tana bukatar a samu izinin iyaye kafin a yi amfani da ita, sannan bayanan da ake samu daga cikinta ba za a iya amfani da su ba wajen talla.

Budaddiyar wasikar na dauke da bayanin da ke cewa: "Manhajar ''Messenger Kids'' za ta iya kasancewa shafin sada zumunta da muhawara na farko da yara da yawa 'yan tsakanin shekara hudu zuwa 11 za su yi amfani da shi.

Bayanin ya kara da cewa bincike da aka gudanar kuma har yanzu ake kara zurfafa shi ya nuna cewa yawan amfani da waya da kwamfuta da sauran na'urori ire-irensu da kuma shafukan sada zumunta da muhawara na da illa ga yara da matasa, wanda hakan ke nuna cewa wannan manhaja za ta iya haifar da matsala ga bunkasar lafiyar yara.

Ya ce, "A takaice kananan yara a yanzu ba su da bukatar samun shafukan sada zumunta da muhawara na kansu.''

"Girmansu bai kai yadda za su iya shiga da jure matsalolin da ke tattare da mu'amullar da ke a shafukan sada zumunta da muhawara ba, abubuwan da kan kai hatta manya ma ga sabani da rikici.''

Sai dai a martanin da Facebook ya yi kan wannan korafi ya ce: "Tun lokacin da muka kaddamar da manhajar a watan Disamba, mun samu sakonni daga iyaye cewa manhajar ta Messenger Kids ta taimaka musu kasancewa da 'ya'yansu ta intanet, kuma ta taimaka wajen sada 'ya'yansu da danginsu na kusa da na nesa.

"Misali, mun samu bayanai cewa iyayen da suke aikin dare sun samu damar kasancewa da kananan 'ya'yansu ta manhajar har suna musu tatsuniya kafin 'ya'yan su yi barci su kuma sun abakin aiki, sannan iyaye mata da suke zuwa aiki wani gari suna samun bayanai kullum daga 'ya'yansu kan halin da suke ciki.''

Wasikar ta bukaci sanin ko akwai bukatar Facebook ya gamsar da wannan bukata, inda ta ce: "Batun wai ana iya magana ko sadarwa tsakanin abokai ko iyaye da 'ya'ya daga wurare masu nisa wannan ba ya bukatar lalle sai an samu wannan manhaja ta ''Messenger Kids''.

"Yara za su iya amfani da shafin iyayensu na Facebook ko Skype ko wasu shafukan su tattauna da su. kai za ma su iya amfani da waya kawai."

Wasikar ta bayar da misalai na bincike da nazarce-nazarce da aka yi da dama da ke nuna alaka tsakanin yawan amfani da matasa ke yi da shafukan sada zumunta da damuwa da kuma zakuwa ko ci-da-zuci.

"Matasan da suke yin akalla sa'a daya kullum suna amfani da shafukan sada zumunta da muhawara kan yi korafi da rashin gamsuwa da kusan dukkanin wani fanni na rayuwar da suke ciki.

"Matasa 'yan makaranta da ke tsakanin shekara 13 zuwa 14, wadanda suke amfani da shafukan sada zumunta da muhawara tsawon sa'a shida zuwa tara a mako, kusan kashi 47 cikin dari ba sa cikin farin ciki kamar takwarorinsu wadanda ba sa yawan amfani da shafin kamarsu akai akai.

Wasikar ta kuma bayar da misalin wani nazari a kan wasu yara 'yan mata masu shekara 10 zuwa 12 wadanda ke damuwa da kibarsu wadanda bincike ya nuna za su iya neman kwaikwayon hanyoyin rage kiba ta intanet.''

Sauran alkaluma na bincike da wasikar ta kawo misali da su sun hada da:
Kashi 78 cikin dari na samari suna duba wayarsu kusan duk bayan sa'a daya
Kashi 50 cikin dari sun ce sun kamu da jarabar amfani da waya
Rabin yawan iyaye sun ce kokarin hana 'ya'yansu yawan amfani da waya ko intanet abu ne da suke fama da shi kullum
Kwarrarun sun kuma karyata ikirarin hukumar Facebook cewa manhajar ta ''Messenger Kids'' na samar da dama maras matsala ga yaran da suke bayar da shekarun karya domin samun shiga shafukan sada zumunta da muhawara, ta hanyar nuna cewa su manya ne.

Kwararrun suka ce: "Yara 'yan shekara 11 zuwa 12 wadanda a yanzu suke amfani da shafin Snapchat ko Instagram ko Facebook ba lalle ba ne su koma kan wata manhaja wadda aka yi ta domin yara.

"Manhajar Messenger Kids ba wai magance wata matsala take yi ba, sai ma dai a ce wata sabuwar matsalar ta kawo,'' in ji masanan.

Kungiyoyin jin dadin yara daban-daban ne suka sanya hannu a kan wasikar, babba daga cikinsu ita ce ta ''Campaign for a Commercial-Free Childhood''. Sauran sun hada da ''Massachusetts American Civil Liberties Union'' da ''Parents Across America''.

Akwai kuma wasu daidaiku da su ma suka rattaba hannu, wadanda sun hada da ''British scientist Baroness Susan Greenfield''.

Gwamnatin Birtaniya ta zauna da kamfanonin shafukan sada zumunta da muhawara da kuma masu yin manhajoji da kwamfuta da sauransu, irin su Apple a watan Nuwamba na 2017 inda ta bukace su da su duba wasu jerin batutuwa kamar:

Yadda za a hana kananan yara shiga wadannan shafuka
Mene ne cin zarafi ta intanet da yadda za a magance shi
Ko akwai yadda za a iya kirkiro wata alama ta gargadi ga matasa waddda za ta rika bayyana a duk lokacin da wani matashi ya dade yana amfani da intanet.


Source By ©Bbc Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user