Wednesday 28 March 2018

Kalli Yadda Wani Ya Kashe Budurwar Sa

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani saurayi dake mataki na uku a Kwalejin koyan aikin Alkalanci da ke Jihar Jigawa, Ringim Ismail, ya bayyana wa ‘yan sandan cewa kin zubar da cikin da yayi wa budurwar sa ‘yar shekara 22 mai suna Salamatu Garba ne ya sa ya yi mata yankan rago.

Ismaila ya ce shekaran su 8 suna soyayya da Salamatu dake zaune a ukunin gidaje na Kofar Gabas dake Jahun, amma sai dai a haka suna tare ne ta dauki ciki. Sun yi ta kokarin su zubar da cikin amma bai yiwu ba har takai wata hudu. Daga nan ne Salamatu ta ce masa baza ta ci gaba ba domin cikin ya girma. Da Isma’il ya tursasa mata, ita kuma taki sai ya ari babur din abonkin sa in da ya dauketa kamar zasu anguwa, ashe inda zai kashe ta ne.

” Bayan mun fita daga cikin gari, sai na kashe babur dina na ko danne ta da karfin tsiya na yanka ta, yankan rago a wuya. Nan take tayi bankwana da duniya.”

Hujjar Ismail dai shine wai don taki ta zubar da cikin da take dashi.

Yanzu dai Isma’il yana tsare a kurkuka, kafin a mika shi ga kotu domin yanke masa hukuncin abin da ya aikata.


Source by ©Premium Times Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user