Wednesday 7 March 2018

Kalli Yadda Wani Saurayi ya Bankawa Gidan Budurwar Sa Wuta Kurmus

Tura Wannan Zuwa Ga
Wani saurayi mai shekaru 27 a duniya mai suna Ifeanyi Ede a yau dinnan Alhamis ya gurfana a gaban alkalin wata kotun Majistare a garin Abuja, babban birnin Najeriya bisa zargin sa da ake yi na cinnawa gidan budurwar sa wuta.

Da yake bayar da ba'asi, dan sanda mai gabatar da kara mai suna Idowu Lawal kamar yadda muka samu tun farko ya bayyanawa kotun cewa shi dai wanda yake tuhumar ya bankawa gidan budurwar sa mai suna Esther Yahaya dake zaune a garin Kubwa, Abuja wuta a ranar 5 ga watan Maris.

NAIJ.com haka zalika ta samu cewa sai dai shi wanda ake karar ya musanta zargin da ake yi masa kafin daga bisani alkalin kotun ya bada belin sa kan kudi Naira dubu 150 sannan kuma ya dage shari'ar zuwa ranar 5 ga wata mai kamawa.


Source by ©Hausa naija
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user