Thursday 29 March 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shugaba Buhari ya gaza ta kowane fanni na shugabancin Nigeria - Fati Muhammad

Tura Wannan Zuwa Ga
Jarumar Ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda ta ce wasu na zagin su kawai domin sun fadi ra'ayin su.

Jama'a da dama sun yi ta mayar wa da tsohuwar jarumar martani inda suka yi kaca-kaca.

Daya daga cikin tsofaffin fuskoki kuma fitattun jarumai a masana'antar shirin fim din Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Fati Muhammad ta fito a wani salo irin na siyasa ta zazzage dukkan abun da ke ran ta game da shugaba Muhammadu Buhari.

Kamar dai yadda muka samu daga wasu kafafen sadarwar zamani, tsohuwar jarumar ta bayyana cewa shugaban kasar ya gaza a dukkan fannonin shugabanci inda kuma ta kara da cewa ba za su ja bakin su suyi shiru ba.

Kamar yadda Muryarhausa24.com ta samu labarin daga  NAIJ.com ta samu cewa jarumar haka zalika ta nuna rashin jin dadin ta game da yadda ta ce wasu na zagin su kawai domin sun fadi ra'ayin su inda ta cigaba da cewa ba za ta yi kasa a gwuiwa ba ko ta dena.

Haka nan ma kuma ta bayyana takaicin ta game da yadda ta ce a shekarar 2015 da suka fito suka nunu kauna ga shugaban ba bu wanda ya nuna masu yatsa amma sai yanzu da suke ganin ya gaza.

Sai dai tuni wasu jama'a da dama sun yi ta mayar wa da tsohuwar jarumar martani inda suka yi kaca-kaca da ita asoshiya midiya din.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Hausa Naija
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user