Monday 23 April 2018

KARANTA KAJI: TUNDA NAKE A DUNIYA BANKO TABAJIN LABARI MAI TAUSAYI IRIN WANNAN BA

Tura Wannan Zuwa Ga

Wata rana wani mutum ya sayi sabuwar mota daga sayanta
yaxo kofar gida yai packing, bayan ya shiga gida ya fito sai ya
tarad da dansa yana rubutu a jikin motar tasa nan take uban
yaron ya hau yaron da bugu
kamar xai kasheshi akan yayimai rubutu ajikin mota...

Ya kama yaron ya daure masa hannuwa ta baya yayimai dauri
GORO, yadaukeshi ya saka a wani daki ya kulle ya tafi da dan
mabudin... Uwar yaron tanata kuka tarasa yadda xatayi ta bude
dakin ta kwanceshi,haka tanaji dan nata yana kuka tun yana
kuka har yagaji ya daina... Bayan wani lokaci mai tsawo uban
xuciyarsa ta sauko sai yadawo domin ya kwance yaron
koda ya bude dakin ya sami dan nasa a sume ko motsi baya
iyayi,nan take ya daukeshi xuwa asibiti..

Bayan likitoci sun kammala
bincike sai suka shaidawa
ubanyaron cewa sai an yanke hannuwan yaro sakamakon
dadewa da yayi a daure...haka
uban yasa hannu a takarda aka yanke hannuwan dan nashi...

Bayan wani lokaci yaron ya farfado daga aikin da akayi masa
sai uban nasa ya shigo domin yaga dan nasa yana shigowa
suka hada ido da yaron,sai yaron ya fashe da kuka yace "BABA
DAN ALLAH KAYI
HAKURI KA DAWOMIN DA
HANNUNA BAZAN KARA MAKA
RUBUTU A JIKIN MOTAR KABA.."
nan take da uban da likitoci da duk wanda ke wajen kowa ya
fashe da kuka.

Bayan mutumin yafita waje sai
ya tsaya ya kalli rubutun da dan nasa yayi da kyau sai yaga
yaron
ya rubuta "I LOVE U DADDY" nan
take uban ya kara fashewa da kuka.

 Ya matsa kusa ga motar ya
taba rubun sai yaga yana gogewa ashe bai lalata paint dain
motar ba Allahu'akbar saurin fushi ke nan.

Allah yasa mu da ce Amin

Source by ©Muryarhausa24.com
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user