Monday 23 April 2018

Karanta Kaji: Daga Yanzu Ni Ba Bahaushiya Bace- Inji Fatima Ganduje

Tura Wannan Zuwa Ga

Fatima Abdullahi Umar Ganduje yar gwamnan jihar
Kano da ta auri dan gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi
tayi tsokaci kan rayuwar aurenta.
Fatima ta kasance matashiya mai shekaru 24 a
duniya, ta kuma kammala karatunta na jami'a da
digiri me daraja ta daya daga jami'ar kasar Amurka
dake jihar Adamawa.

Fatima na da gidauniya data bude dan tallafawa mata
da yara.

A wata tattaunawa da editan City People yayi da ita,
Fatima ta bayyana cewa ita ba Bahaushiya bace, ita
Bafulatanan asali ce.
Game da auren Bayarabe da tayi, tace bata ga wani
banbanci da auren Bahaushe ba domin soyayya bata
san kabilanci ba. Sannan kuma ta jadadda cewa tana
jin dadin rayuwar aurenta domin sirikanta na sonta
suna kuma mutunta ta.

Ta kara da cewa zuwa yanzu ta fara koyon yaren
Yarbanci da ma abincinsu domin ita ma’abociyar son
girki ce.

Source by ©Naija Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user