Wednesday 2 May 2018

DAN ALLAH KUBANI MINTI BIYU KU KARANTA WANNAN NASIHA

Tura Wannan Zuwa Ga


Katashi da wuri yayinda kaji an kira sallah,
kamar yadda idan kaji wayarka tana
Ringing.

ka karanta Al-qurani a nitse, kamar yadda
kake karanta sako idan masoyiyarka taturo
maka.
kaji tsoron Allah, kamar yadda kakejin
tsoron mutuwarka.
katuna mutuwa, kamar yadda kake tuna
sunanka.

Shin kana kulawa dayin sallah akan
lokacinta ???
Mintuna nawa kowacce sallah take ci a
taqaice ???


"Asubah" mintuna 6/8
"Azahar" mintuna 10/12
"La,ASAR" mintuna 10/12
"MAGRIBA" mintuna 7/9
"ISHAA'I" mintuna 10/12

Duka sunacin mintuna 43 zuwa 53 daga
cikin awowi 24 da Allah yake shimfida
mana a kowanne yini da rana ?
Haba 'yan uwana Musulmai ya kamata muyi
tunani akan wannan.

Me muke aikatawa acikin wadannan
awoyi
guda 23 harda mintuna ???
Shin muna baiwa Mahalliccin mu lokutan
bauta masa akan lokaci kuwa ?

"HASBUNALLAHU WA N'IMAL WAKEEL"

Gaskiya muna cutar da kanmu.
Ya Allah kabamu ikon bauta maka yadda ka
umurcemu.

Allah kaji Qanmu, kaji tausayinmu, ka
gafarta mana Amin summa Amin.

Source by ©TAFARKIN TSIRA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user