Wednesday 2 May 2018

Karanta Kaji: Wannan Shine dalilin da yasa Na Kira Matasan Nigeria Cima Zaune kuma Jahilai ko Malalata - Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga


Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karin haske dangane da
jawabin da yai cikin watan jiya a Landan, inda ya bayyana
matsan Najeriya cewa akasarin su sangartattun jahilai ne.

Wannan jawabi ne da ya yi cikin wancan watan ya janyo masa
tsangwama da kakkausan martani daga matasa da magidanta
na kasar nan daga bangarori da dama.

A cikin wata tattaunawa ta baya-bayan nan da Buhari ya yi da
Muryar Amurka, a can kasar a wannan lokaci da ya ke ziyara a
kasar, shugaban ya yi karin hasken cewa:
“A Arewacin kasar nan, akasarin wadannan matasa ba su yi
ilimi ba, ko kuma sun dan fara karatun amma su watsar tun
kafin su yi nisa. Ba don albarkar ruwan damina da muka samu
a damina biyu da ta gabata ba, ai mafi yawan su ba su da aikin
yi, sai zaman-kashe-wando kawai.

“Ire-irin wadannan matasan fa ko da sun je neman kudi a
jihohin kudu, dan abin da su ke samowa bai ma isar su biyan
kudin haya ballantana abinci, sutura da kudin motar komawa
garuruwan su bayan kammala ci-rani.” Inji Buhari.

Ya ci gaba da cewa duk kafafen yada labarai ne suka kara
zuguguta maganar, musamman ma jaridun da ake bugawa a
kullum, saboda su na yin yadda suka ga dama kawai.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din
Muryarhausa24.com don samun abubuwan more
rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin
ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa
Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna
gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Premium Times Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user