Thursday 3 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Mutuwar Jarumar fina-Finan Hausa Hauwa Maina - Muryar Hausa24

Tura Wannan Zuwa Ga


Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Hauwa
Maina, ta rasu a cikin daren nan na
Laraba.

Allah ya yi wa jarumar ta Kannywood
rasuwa ne a Kano bayan ta yi fama da
rashin lafiya.
Shekarun ta sun haura 40.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya ta shaida wa
mujallar Fim cewa Hauwa ta kwanta a
Asibitin Ƙasa (wato National Hospital) a
Abuja na wani taƙaitaccen lokaci.
Daga can ne aka ɗauke ta aka maida ita
wani asibitin a Kano, inda a nan ne Allah
ya yi mata cikawa.
Majiyar ta ce gobe za a yi jana'izar ta a
Kaduna.

Hauwa Maina, wadda 'yar ƙabilar Babur ce
daga Jihar Borno, ta rasu ta bar
mahaifiyar ta, da babbar 'yar ta Maryam da
kuma ɗan ta Abdulrahman.

A shekarar 2017 ne ta aurar da Maryam.
Ta daɗe a harkar fim domin kuwa tun
wajen 1998 ta fara fim lokacin da darakta
Saminu Mohammed Mahmud da ke
Kaduna ya fara saka ta a wani fim da ya
bada umarni.

Daga nan ta ci gaba da fitowa a finafinai,
inda ta kan fito a matar aure.
A cikin shekaru masu yawa kuma ta riƙa
fitowa a matsayin uwa.
Ban da finafinan Hausa, jarumar ta fito a
finafinan Turanci da ɗan dama.
Haka kuma ta shirya finafinai nata na kan
ta a ƙarƙashin kamfanin ta na Ma'inta
Enterprises Limited.

Mutuwar ta ta girgiza mutane a
masana'antar Kannywood.
Allah ya kai haske kabarin ta, amin.

Karin Haske Kan labarin BBC HAUSA 

Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Hausa Hajiya Hauwa
Maina ta rasu ranar Laraba da daddare.
Wani makusancinta ya shaidawa BBC cewa ta rasu ne a Kano
bayan ta sha fama da jinya.
Ana sa ran za a yi jana'izarta ranar Alhamis a garin Kaduna,
inda take zaune gabanin rasuwarta.
Hauwa Maina na daga cikin matan da suka jima suna fitowa a
fina-finan Hausa.

Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna
da zama.

Fim din ta na farko shi ne Tuba wanda Malam Yahya wani
tsohon ma'aikacin gidan talabijin na kasa NTA ya bayar da
umarni
Ta fara fitowa a matsayin budurwa, sai kuma matar aure,
sannan ta koma tana fitowa a matsayin uwa.

A wata hira da ta yi da BBC Hausa da ba a kai ga wallafawa
ba, Hauwa Maina ta ce ba kowane irin fim take amincewa ta
fito ba.
ta ce tana fitowa ne kawai a fim din da ta gamsu cewa
labarinsa ya yi ma'ana, kuma zai ilmantar.
Tuni dai jarumai na fina-finan Hausa suke ta bayyana alhini
dangane da rasuwar jarumar, wacce da dama ke dauka a
matsayin uwa.

Bayan fina-finan Kannywood, Hauwa Maina ta kuma fito a
fina-finan Nollywood na kudancin Najeriya da ake yi da
turanci.

Ita ce ta fito a fina-finai na tarihi kamar Quen Ameena
sarauniyar Zazzau, da sarauniya Daurama .

Hotuna daga shafin muryarhausa24.com

Allah ya kai haske kabarin ta, amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din
Muryarhausa24.com don samun abubuwan more
rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin
ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa
Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna
gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

SOURCE BY ©BBC HAUSA AND FILM HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user