Friday 4 May 2018

Karanta Kaji: Kuskure 10 da akai acikin Film din SAUDAT tare da Sharhin Fim din

Tura Wannan Zuwa Ga


Suna: Saudat
Tsara labari: Shafi’u Dauda Giwa
Producer: Abba Abubakar Babaye
Bada umarni: Falalu A Dorayi
Kamfani: Babaye International Nig Ltd
Jarumai: Adam A Zango, Fati Washa, Rabi’u Rikadawa, Ladidi
Tubless, Fati S.U, Abdullahi Abbas, Nura MC, da Umar But
cut.

Sharhi: Saddika Habib Abba

A farkon fim din an nuna Nabil(Adam A Zango)suna shawara
da yaransa acikin wani katafaren gida shawarar gidan da zasu
fada fashi a ranar domin an nuna kasurgumayen ‘yan fashi da
makami ne a lokacin suka yanke shawarar zuwa gidan wani
babban mai kudi Alh.Mukhtar suka shirya a daren suka tafi
suna zuwa suka tasa shi a gaba da matarsa Hajiya(Ladidi
Tubless) suka ce sai ya fito musu da kudi domin sun sami
labari ya shigo da milyan ashirin gidan, Alh.Mukhtar har fara
gardama amma saboda ya ga da gaske dai kasheshi zasu yi ta
sanya ya dakko musu wannan milyan ashirin ya damkamusu
suka fita daga dakin sannan suka fada dakin wasu ‘yan mata
su uku ‘ya’yan kanwar Hajiya ne suka zo gidan hutu nan ma
suka tsorata su ba tare da sun yi musu komai ba suka fito
suka shiga dakin ‘yar gidan Saudat(Fati Washa) Nabil ya sai ta
ta da bindiga yana tsorata ta amma daya fuskanci babu tsoro a
tattare da ita sai jikinsa ya fara mutuwa Saudat ta tsaya ta fara
yi wa Nabil wa’azi akan abinda yake yi haramun ne domin
Allah baya yafe hakkin wani akan wani ta kawo masa aya da
hadisi ta kashe masa jiki a lokacin ya fara nadamar abinda
yake yi na fashi da makami, bayan ya koma gida sai tunani da
nazari suka shige shi kwata kwata sai ya yi alkawarin ya dai na
sata ya umarci yaransa da su dawo da kudadan daya raba
musu aci-kin wannan milyan ashirin din ta gidan Alh. Mukhtar,
acikin yaransa wasu suka amince kai tsaye wasu kuma sai da
suka bijire masa ba a son ransu ba kowanne yadawo dashi
Nabil yadauka yaje gidan Alh.Mukhtar ya kirawo Saudat ya ba
ta wannan kudi da suka yi fashinsa sannan daga ba-ya ya miko
mata kokon barar soyyayarsa taki amince masa abisa sharadin
cewar sai yaje ya gyara duk barnar da ya yi a baya tare da
alkawarin cewar zai dawo mutumin kirki Nabil ya amince ya
tafi yaje ya fara mayarwa da mutane dukiyarsu daya diba sai
da ya gama kaf yadawo sannan ya fara tsabtatacciyar sana’a
ta halak a lokacinda ya sake dawo wa Saudat yana sake miko
kokon bararsa akan neman soyyayarta Saudat ta amince ita
ma ta fara sonsa amma sai dai kash da ma-ganar tazo gida sai
mahaifinta ya ki amincewa a bisa dalilin cewar ba zai baiwa
‘yarsa dan fashi ba hakan tasa ya kori Nabil
Nabil ya tafi cikin bacin rai kamar yanda itama Saudat take ciki
saboda ta kamu da sonsa sosai itama, kuma kin amincewar
bata saka Nabil ya koma tsohuwar sana’arsa ta fashi ba ya
koma makarantar islama sannan yana cigaba da neman
kudinsa sai daga baya da mahafin Saudat ya yi bincike ya sami
labarin Nabil tuba na gaske ya yi sannan ya kirawo Nabil ya yi
masa alkawarin zai ba shi auren Saudat.

Abubuwan birgewa:

1- Labari fim din ya sami tsari mai kyau

2- An nuna wa al’umma muhimmancin wa’azi da alkairan da
jinsa da aiki dashi hakan yake hai-farwa.

3- An nuna illar abu mara kyau, sannan jaruman sun yi kokari
gurin isar da sakon.

4-Labarin ya tafi kai tsaye bai karye ba har ya dire.

Kurakurai:

1- An sami matsalar daukewar sauti a wasu hotuna na fim din.

2- shin Nabil ba shida kowane yake rayuwa shi kadai? ko iyaye
bashi da su? tunda aka fara fim din ba’a nuna su ba sannan
ko’a baki ba’a fadesu ba.

2- An nuna Saudat yarinyace mai ilimin addini mai tsoron Allah
amma Akwai gurinda aka nuna Saudat tana sallah mahaifiyarta
tazo tana yi mata fadan ta fara harhada sallar ne? shin wanda
yake da wannan halayyar ta yaya za’ayi ya dinga yin sallah ba
akan lokaci ba ballantana har ya dinga harhada wata da wata.

3- A yanda aka nuna Alh.Mukhtar mai tarin dukiya baikamata
ace a gidansa akwai dakin da za’a gani ba’a kawace ba
ballanta har mutum uku a gansu suna barci akan katifa daya
ba.

4- Lokacin da au Nabil suka shigo fashi gidan Alh.Mukhtar
Akwai gurinda suke shigowa dakin ‘yanmata su uku suna barci
sosai yanayin tashin da ‘yanmatan suka yi bai kamata ace
wadanda suke wannan barcin bane domin sun nuna kamar
dama sun san da shigowar su Nabil ne, ya ka-mata ace sun
bari sun dan yi musu wani abu na tsoratarwa sannan su firgita
su tashi.

5- A matsayin Saudat na yarinya mai tarbiyya a lokacin da
Nabil ya kirawota a waya ya fadamata cewar ta fito yana waje
har take cemasa sai ta sanar da iyayenta amma sai mai kallo
yaga bata sanar din ba kuma ta fita wajen nasa.

6-Babu yanda za’ayi dan fashi yashigo gidanka ya yi maka sata
kuma kaga yadawo maka da ita ba tare da ya boyemaka kansa
ba kuma ka aminta dashi lokaci guda dole kayi tunanin wani
abun ya kulla amma sai gashi kaf wanda Nabil ya mayarwa da
kudi babu wanda yaji tsoro ballantana har ayi yunkurin hadashi
da hukuma.

7- Ba’a nunawa mai kallo ba ta hanyar da Nabil yake sanin
sirrikan Saudat ba da duk guraren da ya ke samunta.

8- A matsayin Saudat na yarinya mai tarbiyya baikamata ace
tana soyyaya na tsahon lokaci da Nabil ba har suna haduwa
har a wuraren cin abinci amma duk mahaifinta bai sani ba.

9- lokacin da mahaifin Saudat ya kori Nabil kuma ya yi
alkawarin zai aurar da ita nan da sati daya shin wana dalilin ne
ya hana ba’a aurar da ita din ba domin ba’a nunawa mai kallo
ba sai gashi sai bayan shekara da faruwar hakan ya kuma kiran
Nabil akan cewar ya turo iyayensa.

10- sutturar da aka nuna Nabil yana sakawa lokacin da ya
talauce ba ta dace ba domin suttura ce mai tsada.

Karkarewa:

Fim din ya yi kyau kuma ya kayatar amma tun daga farko
farkon fim din mai kallo ya san abinda zai faru a karshe
saboda an sha yawaita yin ire-iren irin wannan fina-finan a
finafananmu na hau-sa aga mutum yana mugun hali acikin
al’umma amma dalilin mace ya shiryu. Wallahu a’alamu!!!


Hotuna daga shafin muryarhausa24.com


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din
Muryarhausa24.com don samun abubuwan more
rayuwa na

yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://

www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin

Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin

ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me

hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu

Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami

Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin

yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan

masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI


Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa
Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna

gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@

gmail.com mungode


Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin


Source by ©Leadership A Yau and muryarhausa24.com

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user