Friday 4 May 2018

KARANTA YANZU KAJI: TAKAITACCEN TARIHIN KABILAR BABUR DA AL'ADUNTA NA AURATAYYA

Tura Wannan Zuwa


Kabilar Babur tana danganta asalinta ne da Mutanen Yamen,
don haka aka ruwaito cewa rundunar wasu mutane ne sukaƴi
hijira daga Yemen a wajajen shekara ta 600 miladiyya suka
riski Kasar Sudan, sannan suka shigo cikin sahara tare da
sauka a yankin da Kabilar Babur ke rayuwa a yanzu cikin kasar
Borno.

Ba iya kabilar Babur ba, har kabilun Kanuri da Luguda da
wasunsu dake rayuwa a wannan yankin suna ikirarin asalin
kakanninsu daga Yemen suke. Gusawar zamani ne kurum ya
sanya takamaimen tarihinsu ya sauya.
Zuwa yanzu dai, ana samun kabilar Babur ne a Jihohin Borno
da Adamawa.

A jihar Borno, akwai kabilar Babur a garuruwan Biu, Hawul,
Kwaya kusar, Shani, Kwajaffa, Sakwa, Marama, Shaffa,
Wandali, Kida, Miringa, Buratai, Zuwa, Yimirshika ,Hyera
,Dayar, Fumwa, Azare, Gwaski, Diragina, Yimana, Gwallam,
Tiraku, Shindiffu, Goski, Pela Birni, Wangdang, Bula tawewe,
Kogu Tashan Alade, Kida, da hang shang da kuma Bayo,
amma a jihar Adamawa kabilar Babur sunfi yawa a garin
Garkida cikin karamar hukumar Gombi.
Dukkan waɗannan garuruwa da Kabilar Babur ke zaune ciki
nada nasu tarihin.
Misali, ance jarumin daya kafa daular mulki ta Biyu mai suna
Yamta, ɗane ga wata mace 'yar kabilar Mandara.
Wai Tun tana da cikinsa aka ɗauke ta zuwa gidan Sarkin
Borno, don haka acan aka haifeshi kuma acan ya taso da
tarbiyar kanuri.
Amma da Yamta ya girma, sai ya tumbatsa wajen jarumta.
Shine fa harbya karɓe ikon yankin da Biu take ayau tare da kafa
masarauta.

Ana ganin ya fara kafa mazaunin masarautar sane a wani wuri
mai suna 'Limbur@ tsakanin chikorkur da Mandagarau. Har
zuwa yanzu kuma ance kabarinsa yana nan a Limbur ɗin.
Kabilar Babur, sune keda rinjaye a garin Biu da wasu
garuruwan makwabta, amma akwai kuma kabilar Bura wadda
ke zaune a makwabciyar kasar Babur ɗin, mai suna 'Babur
Bura'. Dukkansu kusan da yare ɗaya suke amfani, kuma yaren
yana da kamanceceniya dana garuruwan Chibok, Marghi, Higgi
, Kilba and Bazza.
Anfi samun kabilar 'Babur Bura' a jihohin gabashin Nigeria,
watau Borno, Adamawa, Gombe da Yobe.

AL'ADUN AURE

Mafi yawan kabilun Borno musamman Kanuri, Shuwa Arab da
Babur nada kamanceceniya wajen al'adun auratayya. Watakila
hakan ya faru ne saboda jimawar kabilun wajen zaman tare ko
kuma ana iya cewa kakanninsu ne ɗaya, don haka daga
garesu sukayo gadon ɗabi'un.
Bisa al'ada ta Kabilar Babir, Idan namiji yaga mace yana so, to
bazai sanar mata ba, sai dai ya nemeta da abota.

A wannan abotar ne zai rinka bincikar halayyarta dana
magabatanta, ba tare da ta sani ba, daga bisani kuma sai ya
samu wani dattijo a danginsa ya ɗora masa alhakin kammala
masa bincike akan yarinyar da zuriyarta duka.
Daga wannan matakin kuma sai mai neman auren ya zaɓi
maza uku da mata biyu akalla, daga danginsa su rakashi gidan
su yarinya.
Anan ne zasu haɗu da iyayenta ko 'yanuwanta, har kuma a
tambayeta abinda ke tsakaninsu da wannan mai neman auren
nata, da kuma muradinta akansa da sauransu.
Idan an aminta a kulla auratayya, to daga nan ne za'a sanya
ranar yin Baye, suna kiranta 'Yuyma'.
Idan ranar tazo, dangi zasu haɗu daga ɓangaren namiji da
mace maza da mata a gabatar da kayan ci dana sha, sanna a
sanya ranar aure, watau “Mbwa Nyika”.
Dangane da batun kuɗin aure ko sadaki, namiji na iya bayar da
dukkan abinda ya samu gareshi ga iyayen wadda yake so ya
aura, sukuma zasu ciri wani abu kaɗan su mayar masa da
ragowar, (wasu ma ance basa cirar kome), to amma za'a
gabatar masa da sunayen wasu abubuwa da akeso ya siya
mata.

A hakan ma, ba dole bane ya siyi dukkan komai ba, kawai dai
yana iya zaɓar abinda yake da iko ne ya siya.
Idan namiji ya haɗa kayan, sai ya tashi yan uwansa su tafi
sukai gidan su yarinya. Daga nan kuma za'a saurarar ranar
ɗaura aure.
Daura aure kuwa ya danganta da addinin da mutum yakebi,
kasancewar addini yayi tasiri cikin kabilar Babur, don haka
kiristocin cikinsu sukanje chochi ne domin ɗaura aure, yayin
da musulman cikinsu kan ɗaura aure a Masallatai ko gidaje,
tare da aiwatar da al'adun aure kalar wanda musulunci ya
halatta..

TASIRIN AL'ADAR AURATAYYA GA LAFIYAR SU

1. Kasancewar Kabilar Babur tana da sauki gami da rangwame
wajen kulla auratayya, hakan na ragewa mazajen cikinsu tashin
hankalin fita neman abin duniya ta ko wanne hali domin samun
ɗiyar aure.

Hakan kuwa na iya zamowa abu mafi dacewa dake sasanta
tunanin mazajen gami da raguwar aikata kananun laifuka da
kuma ingantuwar lafiyar kwakwalwa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Sadiq Tukur Gwarzo
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user