Friday 4 May 2018

KARANTA KAJI: LABARIN WANI MATASHI MAI HIKIMA AKWAI DARASI DA NISHADI SOSAI

Tura Wannan Zuwa Ga


Akwai wata qasa da aka taba yi shekaru da
dadewa wadda mutanen kasar suke canza
sarkin su a duk shekara. Kafin mutum ya zamo
sarki a garin, tilas ya amince da tsarin
masarautarsu wanda yace bayan duk shekara,
za'a tura sarki mai mulki izuwa wani daji domin
ya cigaba da rayuwa acan.
Idan lokacin tafiya yayi, sai kaga sarki yaci ado,
ya hau saman giwa, ana zagayawa dashi domin
yin bankwana da mutane. Wannan shine lokacin
bakin ciki ga sarkin da yayi mulki na tsawon
shekara daya. Da zarar an gama kewaya gari
dashi kuwa, sai dakaru su sanya shi cikin jirgin
ruwa, suyi masa rakiya izuwa wannan
kungurmin dajin, sannan su dawo gida abinsu.

A wata shekara, wadannan dakaru a hanyarsu ta
dawowa gari, sai sukaci karo da wani jirgi ya
nutse, amma ga wani matashi ya tsira ta hanyar
riqo da yayi da allon karyayyen jirgin nasu. Da
yake daman suna cikin buqatar wanda zasu
dora sarki na wannan shekarar, sai suka yanke
shawarar suyi awon gaba da wannan matashi
inyaso sai ya zamo sarkinsu na tsawon shekara
daya.
Da fari dai matashin ya bijerewa buqatar sune,
amman daga bisani sai ya yarda. Daga nan nefa
dattijan garin suka labarta masa dokokin
mulkinsu da yadda shima za'a turashi wannan
daji nan da shekara daya. Kwana uku kachal da
dora shi bisa karagar mulki, matashin ya
tambayi dattijan garin ko zasu iya nuna masa
wannan daji inda makomar sa take? Sai suka
amsa masa da eh, suka dauke shi izuwa dajin.
Matashin ya lura da dajin sosai, yaganshi cike da
dogayen bishiyu masu duhuwa, ga kuma kukan
muggan dabbobi nan ko ta ina, sannan sai
qasusuwan mutane wadanda da alama na
tsoffin sarakuna ne wadanda ajalinsu yayi a
wannan dajin wataqila ta hanyar mugayen
namun dajin ko kuma ta rashin abinci.
Shikenan, sai sabon sarkin ya koma gari da
mutanensa. Ya buqaci a samo masa zaqaquran
ma'aikata guda dari zasuyi masa wani aiki. Da
suka isa sai ya tura su wannan dajin, yace yana
so su sare dukkan bishiyoyin dake cikinsa, kuma
su kashe duk muggan namun dajin da suka
gani, shi kuma duk wata zai rinqa kawo musu
ziyara don yaga yadda aikin yake tafiya.

A ziyarar sa ta watan farko, sai yaga cewa duk
namun dajin dake ciki an kashe su, sannan an
sare mafi yawa na bishiyoyin dajin. A wata na
biyu kuwa, tuni aiki ya kammala, daji ya zamo
sarari. Daga nan sai ya umarcesu da su shuka
fulawowi da tsirrai a wasu sassan dajin, sannan
shi dakansa yasa aka kawo dabbobin gida
misalin su kaji da agwagwi, aka ware guri don
kiwatasu. Da wani watan ya kama, sai Sarki ya
umarci a gina masa gida na alatu a wajen. Sarki
ya zamo baya sanya tufafi masu tsada, duk 'yan
kudaden daya samu sai ya tura su daji inda
akeyi masa aiki, ai kuwa a cikin watanni tara sai
ga waje ya zamo wata qaramar alqarya
kyakkyawa.
Daga nan sai ya tara al'ummar gari, yace musu
yana so tun yanzu su aika shi izuwa dajin nan ba
lalle sai ya cika shekara dayan ba. Mutan gari
sukace ba zata yiwuba, dole sai ya cika watanni
ukunsa za'a aika shi wurin mutuwa, basu san
cewa wuri ya zamo na jindadi ba.
Wasa-wasa watanni uku suka cika, akayiwa sarki
kwalliya, aka dora shi bisa giwa ana zagaya gari
dashi, mutan gari na masa jaje tunda zai tafi
gidan halaka, shikuwa baki har kunne, murna
kawai yake abinsa. Sai abin ya daurewa mutane
kai, har ma wani yake tambayarsa da cewa "
duk sarkin da ya riski wannan lokaci zaka
sameshi cikin tashin hankali da qunchi, amma
gashi munga kai walwala kawai kakeyi"
Sai kuwa yayi murmushi, yace "bakaji abinda
masu hikima ke cewa bane? Idan aka haifi yaro,
zakagan shi yana kuka, amma mutane na
murmushi. To idan har yayi rayuwa mai kyau,
sai kaga qarshen sa yazo mutuwa yana dariya,
mutane kuma suna kukan rabuwa dasi. Don
haka ina tunanin irin rayuwar da nayi kenan.
Tunda nahau karagar mulki na raba kaina da
jindadi, ina tunanin abinda zai faru anan gaba.

Hankali na kuma bai kwanta ba har saida na
tsara mafita, kuma nayi aiki tuquru don aiwatar
da abinda na tsara. Shiyasa kaga qarshe na yazo
a wannan gari ina dariya, mutan garin kuma na
kuka. Yanzu gashi na canza dajin mutuwa izuwa
waje na alatu inda zan qarasa rayuwa ta acan."

DARASI

1. Kada ka shagala a wannan duniyar ba tare da
kayi aiki tuquru don gyaruwar lahirar kaba.

2. Ku sani, duk wanda ya zabi raha, hutu da
lalaci a farkon rayuwar sa to haqiqa qarshen sa
zaiyi da-na-sani. Amma wanda ya zabi aiki
tuquru da qoqari, ya hakura da jindadi a farkon
rayuwarsa wajen gina gaba, to tabbas karshen
rayuwar tasa hutu ne da kuma farin ciki.

Allah ya bamu dacewa Amin
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user