Friday 4 May 2018

Karanta Kaji Dalilin sa: Haba Dole ne sai Buhari yayi takara a 2019? To Kusani Ko Yafito bazan zabeshi ba kuma bana farin ciki da sake tsayawar shi takara a 2019 - Obasanjo

Tura Wannan Zuwa Ga


Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ba
zai taba goyan bayan aniyar shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar wa’adi na
biyu ba.

Obasanjo ya kara da cewa sukkanin kalaman da ya furta akan
shugaba Buhari cikin wasikarsa ta ranar 23 ga watan Janairun
wannan shekara inda ya shawarce shi da janye aniyar tazarce
suna nan daram, bai janye su ba.

Tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana haka ne ta hannun
mai nashi shawara akan kafafen yada labarai Kehinde
Akinyemi, yayinda yake karyata rahotannin da ke cewa a halin
yanzu ya janye adawar da yake wa shugaba Muhammadu
Buhari, kuma kari kan haka yana goyon bayan sake tsayawrsa
takara.

Cif Olusegun Obasanjo, ya kuma bayyana rashin gamsuwa
akan ziyarar da shugaban Najeriya Buhari ya kai zuwa Amurka,
wadda ya ce bata amfanawa ‘yan Najeriya komai ba, kuma
koda akwai abin amfanin, bai taka kara ya karya ba.

Yayinda yake tsokaci akan kalaman na tsohon shugaban
Najeriya, mai baiwa shugaba Buhari shawara akan kafafen
yada labarai Femi Adeshina, ya ce, kalaman basu kai darajar
wadanda za a maida wa raddi ba, domin ko kusa basu da
masaniya akan rahotannin da ke cewa a halin yanzu Obasanjo
ya lashe amansa na sukar gwamnatin Buhari, ballantana a ce
ma daga bangarensu aka samu masu yada kalaman.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Rfi Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user