Friday 25 May 2018

Hanya Mafi Sauki da Zaka Bi Ka Sace Zuciyar Duk Wacce Kake So Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga


Soyayya tanada matukar tasiri a rayuwar maza da mata gabadaya, zakayi mamakin yanda masoya ke kula da junansu, idan basu ga juna ko sunji muryar juna ba sai kaga sun kasa samun nitsuwa, wanan shakuwa tanada dalilanta, zakaga wasu masoyan suna soyayya amma shakuwar dasukayi batakai tawasu ba, mekake tinanin yasa haka? Wanan shine abunda zamuyi magana akansa yanzu.

Anan zamuyi magana akan yanda namiji zai sace zuciyar mace. Amfani da kalaman soyayya masu dadi da inganci a lokacin da kake gwagwarmayar samun amincewar zuciyar duk wata yarinya daka gani kakeson mallakarta ko kuma dama kasame ta yanada tasiri sosai a soyayyarku.

Kasance mai lisssafawa tare da tauna dukkan wata magana kafin ka furta mata ita, wannan yanada matukar muhimmanci sabida ance magana zarar bunu ce idan tafita baa dawo daita. Idan kafitar da wanda batada dadi to zaisa kasamu matsala tun farko a tafiyar soyayyarka.

Kada ka kasance mai takura mata akan raayoyinka domin hakan zaisa ta dinga kosawa dakai bata marmarin yin hira dakai, kazama mai yarda da duk abun da zata zo dashi a koda yaushe. Idan zaka yi gyara akan abinda takawo sai kayishi cikin siyasa da wasa yanda zata dauka batare da taji ba dadi ba.

Koda yaushe ka dinga nuna mata tafi duk wata mace kyau a wajenka, duk lokacin da kuke tare ko kukayi waya ka dinga kokarin nuna mata cewa komai nata daban ne, kanuna mata muryarta tafi muryar kowace mace dadi wasu lokutan ma harda dan karya ka kara dashi irinsu “in banji muryaki ba bana iya cin abinci, bana iya bacci” alhali kana cin abincinka kuma kana baccinka, wannan zai sa taji aranta ita tamkar sarauniya ce wajenka.

Soyayya dole saida kyauta, mata suna san kyauta. Kadinga yimata kyauta koda kuwa tafi karfin abunda zaka bata, girma ko tsadan abunda zaka bata bashi bane zaisa taji dadin kyautan, kyauta koda wata iri ce da zaka mata zaisa tagane muhimmancinta a wajenka tasan cewa lallai kadamu da ita. Indai yarinya tanasanka so nagaskiya ko flower ka tsinta a kasa kabata shi a matsayin kyauta zata karbeshi hannu biyu-biyu kuma ta nuna farin cikinta sosai akan wannan kyauta daka mata. Idan zaka iya duk lokacinda da zakaje wajenta katafi mata da wani abu koyaya yake, saidai kuma kada ka sabar mata da bata kudi masu yawa koda yaushe ko abubuwa masu tsada koda yaushe, sabida zata saka aranta kawai kai sai tanada matsala sanan zata nemeka, wanan yazama lokaci zuwa lokaci.

Sanan kada kazama kai kullum saikaje wajenta, kullum saikta ganka, bahaushe ma yace ido wanda yasaba gani ya raina, ganinka yadinga dan yi mata tsada bakoda yaushe zata ganka ba, akalla dai a sati sau daya haka ya wadatar.

Idan kana san mace tasoka sosai kada kazama mai kishi dayawa, mata basa son maza masu kishi dayawa, kada kazama kana takura mata akan abubuwa da basu kai adamu dasu ba, misali daga kaganta da wani sai ka tambayeta wayeshi inta fada maka kacigaba da bin diddigi sai ka gane waye shi mata basa son wannan, ko kuma daga ka ganta ta amsa wayar namiji saikayita takura mata sai ta fada maka waye take waye dashi, da dai sauran irin makamantansu, mata basa san wanan, yana rage ma namiji kwarjini sosai a wajen mace.

Hakuri da kau dakai daga laifin da tayi maka yana kara sa mace tasoka yakuma kara maka kwarjini a wajenta, indai kuna soyayya da mace dole watarana zakuyi fada zata yi maka laifi, hakurin dazakayi da kau dakai alhalin zaka iya daukan wani mataki zaisa ta kara sonka ka kara girma da mutunci a idonta.

Idan kuma kun samu matsala kun yi fada, koda itace tayimaka laifi ka rarrasheta kabata hakuri, wasu maza zakaga koda su sukayi laifi sunajin sunfi karfin su bada hakuri musamman idan suka fahimci ana sonsu, wanan girman kai ne, kuma duk son da kake mata.

Mata nason mulki da mallaka, amfani da shawararta da duk wani abu datace zaisa taji itace mai juya zuciyarka, wanan zaisa takara sonka tadinga jin cewa kai nata ne.

Koda yaushe kadinga fada mata kana sonta, duk da tasan cewa kana sonta amma a duk lokacin da zaka fada mata hakan zaisa taji dadi a ranta, misali bayan kun hadu kun gama hira ko kuma bayan kun gama waya sai katura mata koda sakon waya (text) ne kafada mata kana sonta, ka gwada wanan idan bakayi zakaga yanda zai kara dankon soyayya tsakaninku, irin wadannan abubuwa su zasu saka kasace zuciyarta ta dinga muradin jin muryarka a koda yaushe.

Source: Zinariya
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user