Friday 25 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: An yi fim game da kalaman Buhari kan matasa- Film din Mai Suna Cima Zaune

Tura Wannan Zuwa

An shirya sabon fim game da kalaman Shugaba Muhammadu Buhari da suka ja hankalin matasa a Najeriya. Fim din mai taken "cima-zaune" yana bayani ne game da kalaman da shugaban ya yi cewa da dama daga cikin matasan kasar 'yan-tamore ne kawai, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

A kalaman na watan Afrilu, shugaban ya bayyana cewa mafi yawan matasan Najeriya ba su yi karatu ba, kuma ba su da aikin yi, sannan suna jira gwamnati ta samar mu su abubuwan more rayuwa kyautai.

Wadanda suka shirya fim din sun ce sun yi hakan ne saboda yadda kalaman suka ja hankali a ciki da wajen kasar, sannan suka haifar da ce-ce-ku-cen siyasa.

Furodusan fim din Hamza Lawal Abubakar da aka fi sani da Dogo Dandago, ya shaida wa BBC cewa an shirya fim din ne da nufin fadakar da jama'a game da muhimmacin kamalan shugaban.

Abba Al-Mustapha wanda ya fito a matsayin babban tauraron fim din, ya shaida wa wakilin BBC Pidgin Mansur Abubakar cewa sun lura ne da matsalar cima-zaune a tsakanin matasa a zamanin yau.

Ya kara da cewa sakon Fim din ya bada labarin wani matashi da ya shafe shekaru biyar yana neman aiki da kwalin digirinsa a fannin injiniyarin, amma da aikin ya gagara sai ya zo ya hadu da wasu abokanai da ba a abin da suka sani sai cima-zaune.
"Yawanci za ka ga cewar matasa sun hakura da karatu da duk wasu abubuwa na neman kudi, sun koma suna dogaro da gwamnati da manyan 'yan siyasa," a cewar Al-Mustapha, wanda ya fito a matsayin Rayyan a sabon fim din.

Ya kara da cewa fim din ya kalubalanci irin zaman rayuwar matasa a yanzu tare da fadakar da su kan yadda za su tashi su nemi na kansu ko da kuwa karamar sana'a ce ba lalle sai mutum ya samu aiki ba.

Kawo yanzu ba a bayyana ranar da fim, wanda ake ci gaba da nada zai fito ba.
Ba ya ga Abba Al-Mustapha, akwai karin wasu taurarin na Kannywood da suka fito a fim din ciki har da Sulaiman Bosho.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user