Wednesday 23 May 2018

KARANTA YANZU KAJI: MATSAYIN ZURI'AR GIDAN KAPOOR A MASANA'ANTAR FINA-FINAN INDIA TA BOLLYWOOD

Tura Wannan Zuwa Ga
Tabbas wannan zuria inda akabi tarihi zamuga kowane karni na Bollywood ba Wanda wani Dan gidan baiciki,tundaga uban gayya Wanda shine farko Wanda yafara kafa musu tarihi....

Wannan zuria dai tafara ne da PRITHVI RAJ KAPOORWanda yafara harkar fim tun 1928,an haifi wannan jarumi,mai bada umurni sannan kuma mai daukan nauyi a shekarar 1906...

Yayi finafinai da dama wadanda suka hada harda fim din farko da aka fara magana da waka,duk da abaya yayi wasu sai Mara sa magana....

Wannan jarumi yahaifi yaya uku wadanda suka hada da

RAJ KAPOOR
SHAMMI KAPOOR da kuma
SHASHI KAPOOR..

RAJ KAPOOR


wannan jarumi shine dansa na farko Wanda shima bayan yagirma yagaji babansa Inda shima yakafa tarihi da Dana Wanda baza a manta dashi a Bollywood....

Wannan jarumi kuma shine yahaifi wasu yayan da suma suka gaji sanaar wannan gida....

Yahaifi yaya biyar amma sanannu sune
*RISHI KAPOOR..
*RANDHIR KAPOOR..
*RAJIV KAPOOR.

Rishi yayi finafinai da Dama inda shima yakafa iya nasa tarihin daidai gwargwado Wanda har izuwa Yau ana damawa dashi...
Shi kuma shine mahaifin RANBIR KAPOOR...

RANDHIR shima yayi finafinai kalilan Wanda basu kai na Dan uwansa sannan baisami gagarumar karbuwa ba kamarshi,saidai shima har Yau yakan dan fito awasu finafinai....

Shi kuma shine mahaifin
KARISMA da KAREENA KAPOOR...

RAJIV shima yafara harkar fim kamar yadda yagani agidansu Inda shi bai wasu fim dayawa ba gaba daya fim sha hudu yayi....

SHAMMI KAPOOR


Shine dan Prithvi Raj na biyu kuma kanin Raj kapoor na daya wato SHAMSHER KAPOOR Wanda akafi Sani da SHAMMI KAPOOR ,shima wannan da nasa yataba harkar finafinai kamar mahaifinsa da kuma Dan uwansa inda yai finafinai da dama inda shima yabada mamaki sosai kamar dan uwansa...

Shi kuma yayansa biyu Wanda daya ne kawai yabiyo gadon gidan saidai da yake yafi bada karfi wajen directing shiyasa baza a sanshi sosai ba sunansa ADITYA RAJ KAPOOR...

Aditya yayi mataimakin maibada umurni a manyan fim wadanda suka hada da SATYAM SHIVAM SUNDARAM,GIRAFTAR,SAAJAN da dai sauransu.....

SHASHI KAPOOR...


Wannan jarumi shine Dan PRITHVI RAJ KAPOOR na uku duk da shi prithvi din yahaifi wasu dasuka mutu abaya to wannan dai shine autansu...

Kamar yadda muka sani shima shashi yayi manyan finafinai da dama wadanda suka hada da SHAAN,KABHI KABHI da dai sauransu....

Yasami karbuwa sosai kafin yai retire,shi kuma yayansa uku gaba daya wadanda suka hada da
KUNAL ..
KARAN sai
SANJANA..

Kunal shima ya dauko hanyar gadon gidan su saidai rashin daukaka tasa yayi baya da harkar inda bayan yayi finafinai shida yakoma mai daukan nauyi baitashi dawowa ba sai a SINGH IS BLINGH na jarumi AKSHAY KUMAR....

Kaninsa Karan kuma shima yaso dauko gadon gidansu saidai shi kalarsa tasa yai baya domin mahaifinsu baturiya ya aura inda suka dauko kalar turawa,karan yayi biyar kawai sai kuma TV shows dayayi daga ciki nasan wadanda suka jima suna kallo bazasu manta da LOHA ba to shine Dan baturen nan Dan soyayya....

Kanwarsu kuma wato SANJANA itama tadan tabo gadon gidansu inda tayi fim naturanci daganan kuma takoma aiki under theater....

To wannan shine atakaice idan ku kayi dubi zakuga tabbas sunfi kowa yawa a masana antar Bollywood sannan sune asalin yan gado....

Ga jerindsu
Prithviraj Kapoor
Raj Kapoor
Shammi Kapoor
Shashi Kapoor
Randhir Kapoor
Rishi Kapoor
Rajiv Kapoor
Karan Kapoor
Kunal Kapoor
Sanjana Kapoor
Karisma Kapoor
Kareena Kapoor
Ranbir Kapoor

Sannan wani abin mamaki suna da alaka mai karfi da wasu zuriar a Bollywood..

Kamarsu
Bachchan family
Nath family
Da sauransu....

Dafatan wannan tarihi ya kayatar daku....

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Fim Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user