Wednesday 23 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Dalilin Da Ya Sa Cutarwar Kwakwalwa Ta Fi Ta Jiki

Tura Wannan Zuwa


Wani kwararre a harkar lafiya kuma ta bangaren halayyar mutane Farfesa Mr Adedotun ya ja kunnen mutane dangane da, idana ka batawa mutum rai, iri haka na iya samar da wata babbar cutar da zata iya kawo matsaloli.

Ajiboye yana aiki ne a asibitin koyarwa na jami’ay Ado- Ekiti ya bada wannan shawarar ce ko kuma jan kunne, lokacin da yake hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya. Ya ce, wasu abubuwan da za a yi ma mutum domin a bata mashi rai, zasu iya kasancewa ta hanya daban daban.

Kamar yadda kara bayyanawa shi al’amarin bata rai, yana iya kasancewa ne akan daya daga cikin wadannan, fyade, ko da baki, ko kuma da karfi, yayin da kuma shi dayan duk bai kunshi su abubuwan da aka fara magana akansu ba.

‘’Maganar yadda za a wulakantar da mutum ba kamar yadda za a ci mutuncin mutum bane ta hanyar karfi, don haka mutane da a na iya kasancewa cikin wannan hali, su yi shekaru ba tare da sanin wani ba’’.

‘’Abin ba za a iya lura da shi ba har sai an fara ganin wasu abubuwan da basu kamata ba, daga wani lokacin da abin ya fara nuna kan shi.’’

‘’Ajiboye ya nuna cewar a lura sosai shi al’amarin daya shafi din zarafin mutum da kuma wulakantwa, hakan yana iya samar da, yanayin da zai sa a rika jin tsoro, da kuma shiga halin kagara.

’’Tsoro wani irin yanayi wanda mutum ne ke shiga , saboda yadda hankalin shi ke ciki, ko kuma yadda aka yi amfani da karfi, abin na iya shafar lafiyar shi.

Ya kara jan hankalin cewar shi al’amarin tada hankalin mutum yana iya kawo rashin lafiyar jiki, kamarsu zuciya da dai sauransu.

’’Cardiobacilar su kuma cututtukan suna da alaka da hawan jini da kuma mutuwar bangaren jiki, yayin da shi kuma gastrointestional yana iya samar da gyambon ciki wato ulcers. Akwai abinda zamu iya kira abubuwan da shiga wasu yanayi ke samar dasu wanda magani ba zai iya shawo kan al’amarin ba.

Masanin halayyar dan Adam ya ce,shiga irin halin yana shafar mutum ya kasa hulda da mutane, saboda halin da aka say a shiga, irin haka na kai gas a mutum ya kauracewa mutane.

Ya lissafa wasu abubuwan da zasu iya samar wanda ya ke cikin irin wannan halin , sun hada da psychosis, gajiya, rashin barci, halin ko in kulak an abubuwan da suke faruwa, wannan na sa mutum yaga kamar kowa ma ya tsane shi, daga karshe yana iya kashe kan shi.

Ajkiboye ya kara jaddada cewar babbar janyar da za abi saboda ashawo kan yadda aka wulakanta wani, ita ce, a samu amincewa da yarda cewar da akwai matsalar.

Ya kuma bada shawar fa wadanda suka shiga irin wannan halin da su rika fadawa mutane, ko dai malamai ko kuma shawara daga masana bangaren lafiya.

‘’Samin shawarar wadanda suke da ilmin da ya shafi kiwon lafiya yana da wuya a cikin al’umma na yanzu’’.

Wanda kuma ya san ana takura ma shi har abin ya kai ga sa ran shi ya baci, sai yayi kokari kada ya kasance a wurin da ake yi ma shi hakan, musamman ma idan aka lura abin ya fara shafar lafiyar shi.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user