Thursday 31 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shin dagaske ne an gayyaci Adam A. Zango Kasar Faransa domin Gabatar da Wasan Sallah???

Tura Wannan Zuwa




Shararen jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam Zango, zai tafi kasar Faransa domin hallartan nadin sarauta da za'ayi wa wasu hausawa mazauna kasar inda kuma ake sa ran zaiyi wasa a wajen taron.

Kamar yadda jaqridar Premium Times ta ruwaito, Zango zai yi waka a taron da za ayi a ranar 23 ga watan Yuni na 2018 wanda zai samu hallartan hausa daga ma wasu kasashen turai.

Likafa ta cigaba: Adam Zango zai yi wasa a kasar Faransa


"Ina murnar sanar da ku masoya na cewa an gayyace ni zuwa nadin sarauatan wasu muhimman mutane da hausawa mazauna kasar Faransa za su dauki nauyin gudanarwa.
"Za'a karama mutane da dama daga kasashen Kamaru, Chadi, Jamhuriyar Congo, Ghana da kuma wasu kasashen turai kuma ina daga cikin wanda aka gayyata don inyi waka a wajen taron," inji shi.

Masoya jarumin sunyi tururuwa zuwa shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram don taya shi murnar wannan karamci da akayi masa tare da yi masa fatan alkhairi.
Zango yana daya daga cikin jaruman Kannywood da su kayi fice wajen wakokin Hausa wanda hakan yasa wasu ke yi masa lakabi da 'Davido na Arewa' inda suke kwatanta shi da shahararen mawakin Najeriya Davido.
Baya ga haka Zango ya sami nasarori sosai a matsayinsa na jarumin fim da kuma mai shirya fina-finai. Wasu daga cikin fina-finansa da su kayi farin jini sosai sun hada da Basaja da Gwaska.
A shekarar 2016, Zango ya samu rashin jituwa da jaruma Rahama Sadau inda su kayi ta musayar maganganu amma daga baya Sadau ta shaidawa majiyar NAIJ.com cewa tuni sun shirya da Zangon.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Hausa Naij
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user