Thursday 31 May 2018

KARANTA YANZU KAJI: LABARIN WANI SAURAYIN DA YAKE TURA SAKO NA EMAIL 'DIN BATSA DAGA KABARIN SA -WANNAN LABARIN YA GIRGIZA NI MATUQA

Tura Wannan Zuwa

Wani mutum yake ba Dr.
Muhammad
Abdurrahman Al-arefe na
kasar
Saudiyya labarin wannan
abin da ya
faru.

Mutumin yana cewa:
Ina da wani aboki ya mutu,
sai wani
abu ya biyo bayan mutuwar
sa, ina
fatan Allah ya jikan sa, kuma
ya rinjayar
da ayyukan sa na Alkhairi
akan
ayyukan sa na sharri, ba wai
mutuwar tasa bace babbar
matsalar da ta dame
ni ba, domin ko wannen mu
zai mutu,
sai dai babban damuwan da
ke cikin
mutuwar ta sa itace:

"Yana da wani mugun aiki
dake
gudana ta email dinsa,
wanda tun yana da rai ya
kasance yana son website
dinda suke yada hotunan
batsa. Har ma
sai da yayi tarayya da wani
website na
'batanci, ya biya su kudi
suna tura masa
da batsa lokaci bayan lokaci.
Har ta kai
ga ya 'kara biyan wani kudin
tare da bada email din
abokan sa don a dinga
tura masu da hotunan batsan
da sunan
shi, da kuma kudin sa, a duk
sanda
wannan website din suka
samu wani
sabon batsa.

Kwasam! sai ya mutu, kuma
babban
abin damuwa shine ba
wanda ya san
number sirrinsa na wannan
website ko
email din domin mu tsayar
da wannan
sakon da ake aikawa mutane
da sunan
sa, na tsaya ina ta tunanin
yanda za’ayi, alhalinkuma ina
cikin masallaci ina jiran
ayi masa sallar gawa, bayan
an yi masa
sallah aka dauke shi a kafada
muna
tafiya zuwa makabarta, sai
wani tunani
ya fado min yanzu me
wannan bawan
Allah zai gani a kabarinsa...

Hotunan batsa?

Hasbunallahu wa ni’imal
wakeel.

Bayan mun kai makabarta, na
duba
kabarin da za’a birne shi, na
sake duba
cikin kabarin Hmm! Yanzu
ya yanayin
sa zai kasance a cikin wannan
kabarin?

A kewaye da kabarin kuma
ga mutane
suna ta kuka, bayan mun
birne shi muka barshi a cikin
duhun kabari shi
kadai, sai mu da ‘yan uwansa
da
dukiyarsa muka juya zuwa
gida, ba
abinda ya sauran masa face
aikin sa.

Bayan haka sai mahaifiyarsa
ta yi
mafarkin yara suna zuwa yin
fitsari
akan kabarin sa, abin ya
daure mata
kai, sai take bamu labarin
abin da ta
gani a mafarkin kuma tana
son ta san
meye ma'anar wannan
mafarkin, ita kuma uwar bata
san labarin abin da
yayi kafin mutuwarsa ba, sai
na fadi a
zuciyata: Ai wannan mafarkin
baya
bukatar neman fassara domin
ma’anar
sa a bayyane take, wainnan
yaran da ta
gani a mafarki suna zuwa yin
fitsari a kabarinnasa, sune
mutanen nan da
suke tura masa hotunan
batsa da shi
da abokanen sa, Ya Salam!

Yanzu ya zai
iya daukan nauyin wainnan
laifukan?

Ya zayyi da nauyin nasa
ballantana har
da na abokanen sa?

Nayi Kokarin na kyautata
masa, sai na
kira website din da suke turo
masa da
abokansa wainnan abubuwa
na batsa,
don su tsayar da turo masa
da wainnan
sakunan,su kuma cire shi
cikin wannan
tsarin, sai dai basu yardaba,
kuma suka nemi uzuri a
wajena, suka ce ai duk
wanda ya shiga tsarin yana
da number
sirrinsa don haka na basu
number, Na
ce masu Shi mutumin ya
mutu!!! Ko
kulani basu yi ba.

Na zauna ina ta tunanin
wane irin hali
yake ciki yanzu! Sai na tuna
da Hadisin
da Manzon Allah (SAW)
yake cewa:
"Lallai daga cikin mutane
akwai masu
rufe alkhairi kuma su bude
sharri".

Kai! ina tunanin shima
wannan bawan
Allah yana cikin su, sau nawa
nake ta yi
masa fada, amma yaki dauka.

Ina ce
masa: "Shin zaka iya daukar
nauyin
zunuban mutane? Ya zaka
zama
mabudin sharri? Ya zaka
dauki nauyin laifin da suka
aikata a wuyanka ranar
Alqiyama? Sai dai a wannan
lokacin
yaki karban nasiha ta, yana
ganin ai shi
matashi ne, kuma ma
wannan ai don
'debe kewa ne, Subhanallahi!
mutane
nawa ne cikin matasa suka
kalli wani hoton batsa kuma
suka abkawa
alfahsha sanadiyyar haka?
Labarin sa ta
kare".

Da wannan ne ni kuma nake
cewa muji
tsoron Allah, mu gyara
ayyukan mu,
kuma duk wani page din da
muka yi
liking muka san cewa na
batsa ne ko
kuma suna sa hotunan batsa
wani
lokaci da mu fita daga
wannan page din, saboda
bamu san sanda zamu
mutu ba, kuma mun san ba
wanda
muka sanar dashi password
din mu,
kamar dai yanda muka ji ya
faru ga
wannan bawan Allah din.

Kullum
Malamai kokarin farkar da
mutane suke yi musamman a
Facebook amma
mutane suna daukan sa wasa
sun
manta abin da Allah yake
cewa:
((Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar
da matattu
kuma Mu rubũta abin da
suka gabãtar,
da gurãbunsu, kuma kõwane
abuMun
ƙididdige shi, a cikin babban
Littãfi
Mabayyani))

Allah kuma Ya sake cewa:
(Rãnar da Allah zai tãyar da
su gabã
daya, sa'an nan Ya bã su
lãbãri game da
abin da suka aikata, Allah Yã
lissafa shi,
alhãli kuwa sũ, sun manta da
shi, kuma
a kan kõme Allah Halartacce
ne).

Muryarhausa24.com

Manzon Allah (SAW) yace:
"Duk wanda
yayi kira ga aikata abin da
Allah ya
hana, yana da girman zunubi
kwatankwacin duk wanda ya
aikata
wannan aikin,kuma ba za'a
rage masa
komi a cikin laifin ba Kuma
kowanen mu za’a tambaye
shi a ranar Alkiyama
kan ko wane abinda ya kalla
na
Alfahsha ko kuma ya abka a
cikin ta
ko kuma wani hoton batsa
daya yada
ta a cikin Al’ummah, bana
tunanin
zamu iya daukan wannan
nauyin laifin.

Sai daina rokon
Allah ya shirye mu

Dan Allah kuyi Share din
wannan Labarin Saboda
Jama'ar Musulmi
Su Amfana gaba daya
Allah Yasa Mu cika Da Imani Amin

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Muryarhausa24.com
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user