Thursday 31 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Wani Dan sandan Indiya na fuskantar barazana don ya ceto Musulmi

Tura Wannan Zuwa Ga


'Yan sanda a Indiya sun ce jami'in dan sandan nan da ya sha yabo saboda jarumta da ya nuna lokacin da ya hana wani gungun mabiya addinin Hindu kona wani Musulmi, yana fuskantar barazana ga rayuwarsa.

Tauraruwar Gagandeep Singh, wanda jami'in dan sanda ne a jihar Uttarakhand ta haskaka bayan da aka wallafa hoton bidiyo da ya nuna lokacin da ya ceto wani Musulmin daga hannun wani gungun mutane a makon da ya gabata.

Mutumin ya kai ziyara ne wani wurin ibada na mabiya Hindu tare da budurwarsa wacce take bin addinin Hindu.

Gungun mutanen sun yi masa kawanya inda suka yi kokarin far masa, kuma sun zarge shi da "yin jihadi ta hanyar amfani da soyayya".

Kalma ce da kungiyoyi masu tsatstsauran ra'ayin addinin Hindu suke amfani da ita wadanda suke zargin maza Musulmi da sauya ra'ayin mata mabiya Hindu ta hanyar soyayya.

Lokacin da bidiyon al'amarin ya fara bayyana a shafukan sada zumunta, mutane da dama sun kira Mista Singh "mutumin da za a yi koyi da shi " kuma jaridu da dama a kasar sun wallafa labarin.

"Ina aikina ne kawai. Ko da ban sanya kayan sarki ba, zan yi abin da da na yi kuma ya kamata kowane Ba'indiye ya yi haka," in ji shi.

Sai dai kuma ba da jimawa ba ne mutane suka fara sukar matakin da Mista Singh ya dauka, inda suke zarginsa da kare "sabuwar dabi'a".

Jami'an 'yan sanda da suke aiki tare da shi sun ce an rika tura masa sakonnin barazana ga rayuwarsa.

Sai dai wadansu 'yan siyasa a bainar jama'a sun ce gungun mabiya Hindu ba su aikata laifi ba.

"Ba daidai ba ne maza Musulmi su rika zuwa da mata mabiya addinin Hindu zuwa wuraren ibadanmu duk da cewa sun san cewa wurin ibada ne, mai tsarki,"in ji Rakesh Nainwal, mamba a jam'iyyar BJP mai mulki.

Sai dai wadansu mazauna unguwar Ramnagar, inda a nan ne lamarin ya faru sun ce al'amarin yana tayar da hankali.

"Idan saurayi da buduwarsa sun je wani wuri tare, shin me ya sa kungiyoyin masu tsatstsauran ra'ayi za su kira shi da yin jihadi ta hanyar amfani da soyayya tare kuma da kai musu hari " in ji Ajit Sahni, wani mazaunin Ramnagar.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user