Thursday 31 May 2018

Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Marigayi Ali Banat - Waye Wannan Ali Banat din da ake Magana Akai?

Tura Wannan Zuwa Ga


Matashi Ali Banat mazaunin birnin Sydney dake kasar Australia ne, Musulmi ne daya hadu da cutar Cancer mai karfin da likitoci suka shaida masa cewa bazai shige wata bakwai a duniya ba, a nasu binciken sai dai hukuncin Ubangiji ya canza masa raahin lafiyar....

Bayani daya samu daga likitoci ne ya sanyashi gaggawar kokarin kyautar da dukkan dukiyar dayake da ita, ta hanyar temakawa mabukata musammam a yankin aftica....



Kafin bayyanar cutar dake damunsa Dan kwalisar matashi ne dake gudanar da rayuwar masu kudi kamar dai yadda wasu matasan keyi idan Suna da kudi, ya Mallaki Mota Ferrari Spider mai tsadar tsiya, wacce ba kowanne matashi bane ke iya mallakarta, yana da kayan sawa na alfarma, tare da agoguna masu tsadar gaske, kusan dukkan abubuwan da Ali ke amfani dasu suna da daraja, amma cikin rahamar Ubangiji sai ya nufeshi da bin hanyar temakawa mabukata da dukiyarsa....

Ali Banat ya gina Masallaci tare da makarantar koyar da addininmusulunci anan africa, ya rabawa talakawan africa kayan sawansa tare da bayar da kyautuku masu tsoka ga wadanda Allah yasa suke da rabo daga dukiyarsa....



Banat ya bayyana cewa Kyauta ce ta musammam da Allah ya bashi wacce zaiyi amfanj da ita wajen nemawa kansa kusanci ga mahaliccinsa, yace badon bayyanar cutar ba, zai cigaba da more kayatattun abubuwan dake duniya ne, ba tare daya tunanin mutuwa zata dauke shi a cikin kuruciya ba, amma sanin cewa Watanni kadan suka rage masa hakan ya temaka masa wajen karasa rayuwarsa ga aikata ayyukan alherin daya faranta zukatan wasu al,umma dayawa a duniya, adduarsa itace Allah ya karbi wannan aiki nasa kuma ya yafe masa laifukan daya aikata......

Ali yakan yawaita ziyartar Makabarta a kowanne lokaci, don hakan ya kara tunasar dashi lokacin zuwansa cikin kabari yana gaf da zuwa....




Ali Banat ya rasu a kwanakin baya kadan da suka shige, amma yayi nasarar kyautar da kusan dukkan dukiyar daya mallaka, kuma ya saka farin ciki a zukatan al,umma masu yawa a duniya...

Allah ya gafartamasa tare da sauran musulmi Amin


Gareku wayanda baku sanshi ba, Jiya Talata Allah (Swt), ya
karbi Ransa bayan ciwon daji na makura ya kamashi a duk
sassan jikinsa (Wadda a turance ake kira da da stage 4
cancer), Cutar dajin da ta wuce misali wacce idan Cutar daji
takai wannan matsayin da wuya mutum ya rayu. dama ya
kasance matashi mai Arziki kuma mai hidimtawa marasa
galihu da dukiyarsa.

Watanni kalilan kafin wannan wata likitoci suka tabbatar masa
da Cutarsa tayi nisa don haka da wuya Ya kara Watanni masu
yawa anan gaba.

Ali wanda tun kafin a sanarda shi wannan ya mika rayuwarsa
da dukiyarrga kacokan ga marasa galihu musamman na
wannan yanki namu afrika, inda yakan gina musu gidaje tare da
rijiyoyi da sanya 'ya'yan marayu makaranta da sauran ayukkan
alkheri. kuma Ali har ya bar wannan duniya jiya kenan wannan
shine aiki da yasa a gaba.
Kafin Mutuwarsa dai ya fitarda wani tsari na taimakawa
musulmin da basuda karfi na duk duniya wanda ya sanya masa
take, MATW Project (wato Muslims Around The World).

Babu shakka wannan Wa'azine garemu Idan zamu hankalta mu
taimakawa marasa galihu domin wata rana bama wannan
duniyar kuma abinda mukayi sadaka shi zamu gani a CIKIN
QABARI DA GOBE QIYAMA. Allah yajikan ka Ali kaida dukkan
Musulmi.




Takaitaccen Tarihin Shehu Usman Ɗan Fodio : Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Mujaddadi Shehu Usman Ɗan Fodio - Hotuna da Cikakken Tarihi

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Rabi'u Biyora and Jamilu Sani Rarah Sokoto

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user