Thursday 26 July 2018

DAN ALLAH 'YAN UWA NA KU DUBI WANNAN SOYAYYA

Tura Wannan Zuwa Ga
KU DUBI WANNAN SOYAYYA


Yayin da aka idar da yaqin Uhudu, Sai Manzon Allah (saww) yace ma Sahabbansa (ra) "WA ZAI DUBO MIN ABINDA YA SAMU SA'ADU BN RABEE'U?".

Sai wani daga cikin Sahabbai ya tashi ya tafi yana duddubawa acikin Matattu (Ko zai ganshi). Amma sai shi Sa'adu din ya riga ganinsa tun kafin fitan ransa.

Don haka ya kirashi yace masa "Me kake yi?". Sai yace "Manzon Allah ne (saww) ya turoni domin in duba shin wanne hali kake ciki?".

Sai Shi Sa'adu bn Rabee'a (ra) din yace "Ka isar da gaisuwata zuwa ga Manzon Allah (saww) sannan ka bashi labarin cewa ni na Mutu. Kuma cewa ni an sokeni (Da Mashi) sau goma sha biyu, Kuma an cim mani. Don haka ni mutuwa zanyi babu makawa".

"Kuma ka isar min da gaisuwa zuwa ga Mutanena, Kuma kace musu "Ya Ku Mutane! Hakika baku da wani Uzuri (awajen Allah) idan har kuka bari aka ta'ba Manzon Allah (saww) alhali acikinku akwai wani ido mai motsi".

Da ya gama fa'dar wannan Muhimmiyar wasiyyah shikenan sai ruhinsa ya fita ya koma ga Ubangijinsa (SWT).


DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

ALLAHU AKBAR!!! ALLAHU AKBAR!!!
'Yan uwa Kunji fa Sahabbai Mutanen kirki.

 Aikinsu Annabi, Rayuwarsu Annabi, Tunaninsu Annabi, Mutuwarsu ma saboda Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Gaskiya duk wanda zuciyarsa take da hasken Son Manzon Allah (saww) zai yi wahala ya karanta wannan Wasiyyar bai zubda hawayen idanu, ko kuma na zuciya ba.

Ya Allah ka saka ma Sahabban Annabinmu da alkhairi baki dayansu. Ka Qara yardarka garesu, ka Qara musu daukaka afadarka. Ka yarda damu muma don albarkarsu. Ameen.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user