Thursday 9 August 2018

Kalli Sababbin Hotunan Jarumi Rabi'u Rikadawa Cikin Shigar Mata a Wani Sabon Film

Tura Wannan Zuwa Ga
Hotunan Fitaccen Jarumin Fina-Finan Hausa Rabi'u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila sun ɗauki hankula Sosai.


Rabiu Rikadawa yayin ɗaukar Kwalliya

MuryarHausa24.com.ng ta shahara wajen kawo muku labari akan abinda ke wakana a farfajiyar Kannywood a Yau muna tafe da Labarin Rabi'u Rikadawa kamar yadda sunan shi yake ba ɓoyayye bane a Masana'antar Hausa Films.

Nasir Makeup ne ya tsara  Kwalliyar

Rabi'u Rikadawa ya kasance Jarumi mai fitowa a matsayin Mahaifi (UBA) a cikin Fina-Finan Hausa kana ya kasance Shahararre a farfajiyar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood.

Ainihin Hotan Rabi'u Rikadawa

An saki sababbin Hotunan a shafin Instagram yayin ɗaukar wani fim mai suna KARAMIN SANI  wanda ba'a kammala ɗaukar shirin fim ɗin ba a halin yanzu.

Wannan dai ba shine karo na farko da jarumin ya fito a siffar mace ba ya fito a fim waɗanda zamu iya cewa sun shahara kamar irin su ADON GARI, KARA'I da sauran su.

Shirin Karamin Sani

Fim ɗin ya samu umarnin Jarumi kuma Mai Bada Umarni Falalu A. Ɗorayi cikakken bayani yana nan zuwa akan fim ɗin kai dai ci gaba da kasancewa da Shafin MuryarHausa24.com.ng a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

Fitaccen mai yin kwalliya a masana'antar Shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD) Nasir Makeup ne ya shirya masa wannan kwalliyar wanda a karon farko ba lallai bane ka gane Namiji bane.


Fatima ɗiyar Rabi'u Rikadawa

Idan ba zaku manta ba a watan January ɗaya daga cikin 'ya'yan Jarumin  mai suna Fatima ta sauke  ALƘUR'ANI MAI GIRMA .

Ku ci gaba da Kasancewa da shafin mu a www.muryarhausa24.com.ng domin samun takaitaccen Tarihi Rabi'u Rikadawa dama sauran muhimman batutuwa da suka shafi masana'antar shirya fina-finan Hausa (KANNYWOOD) dama Duniya baki ɗaya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user