Monday 27 August 2018

Karanta Labarin Fim din da ba'a Taba Yin irin shi ba a Tarihin Kannywood

Tura Wannan Zuwa Ga
A jiya ne kamfanin shirya finafinai na Kwankwaso ya saki tallan sabon fim dinsa mai suna Ba Kama a kafafen sadawar zamani, domin dai a bi tsari da duniyar finafinai ke tafiya a kai. Fitar wannan tallan ya janyo hankalin dubunnan mutane ma su sha’awar kallon finafinan Hausa.


Tallan fim din ya kayatar da mutane matuka da gaske, musamman da yake an ga sabbin abubuwan da ba a saba gani a Kannywood ba.

Kwankwaso Movies, Kamfani ne da ya samu sahalewar hukumar ba da lasisin Kamfanoni ta ƙasa, kuma yana ɗaya daga cikin Kamfanonin da suke samar da ingantattun fina-finan Hausa don amfanin jama’a maza da mata.

Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya fina-finan Hausa wato tsangayar Kannywood, ya kwana da sanin samun sabon canji da ake kokarin samarwa duba da yadda sauran masana’antun samar da fina-finai na duniya suke a kan tsari na ci gaba a ko da yaushe, don haka wasu daraktocin ke ganin bai dace muma a bar mu a baya ba.


Shi dai wannan fim mai suna Ba Kama, yana ɗauke da salon na musamman wanda zai ƙayatar da al’umma, kasancewar an yi amfani da ƙwaƙwalwa wajen tsara zubin labarin da kuma jaruman da za su fito a cikin fim ɗin.

Da yake zantawa da wakilinmu game da fim ɗin, Darakta Yaseen Auwal ya ce, haƙiƙa fim din an daɗe ba a ga irinsa ba, domin ya sha bamban da irin finafinan da suke fitowa kasuwa yanzu. A cewarsa, tsarin da aka bi na ɗaukar fim ɗin da kuma kasuwancinsa ba kamar yadda aka saba gani ba ne.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user