Monday 27 August 2018

Karanta Kaji: Kuskure 6 da akai acikin Film din MARIYA tare da Sharhin Fim ɗin

Tura Wannan Zuwa Ga
Suna: Mariya

Tsara Labari: Fauziyya D. Sulaiman da Ali Nuhu

Kamfani: Mai Shadda Inbestment

Shiryawa: Abubakar Bashir Mai Shadda

Umarni: Ali Nuhu


Jarumai: Ali Nuhu, Jamila Nagudu, Maryam Yahya, Ladidi Fagge, Garzali Miko, Umar M. Sharif, Baballe Hayatu, Hadiza Muhammad, Abdu Karkuzu. Da sauran su.

Sharhi: Hamza Gambo Umar

A farkon fim din an nuna Yawale (Garzali Miko) tare da tawagar abokan sa ‘yan daba suna tafe rike da mugayen makamai, ganin su ne yasa Abdullahi (Umar M. Sharif) Ya garzaya a guje yaje gidan su Mariya (Maryam Yahya) ya sanar da mahaifiyar ta Habiba (Ladidi Fagge) tahowar su Yawale da mugun nufi don su hallaka Mariya. Jin hakan yasa Mariya tabi ta bayan gidan ta gudu yayin da saurayin ta Abdullahi yabi bayan ta suka bazama cikin daji. A wannan lokacin ne Yawale da gayyar abokan sa ‘yan daba suka iso gidan su Mariya suna neman ta, ganin basu ganta bane yasa suka cinnawa gidan wuta sannan suka fita, a sannan ne wani saurayi ya fada musu hanyar da su Mariya suka bi, nan suka bi bayan su Mariya wadda ta sanar wa da Abdullahi tana jin ‘kishirwa, hakan yasa ya bazama cikin daji yana neman ruwa, kafin ya dawo su Yawale sun kusa isowa wajen da Mariya ta buya, amma sai wani maciji ya biyo su hakan yasa suka gudu. Ganin sun gudu ne sai Mariya ta cigaba da gudu, amma sai tayi kicibus da abokan Yawale ‘yan daba, har sun yi yunkurin cutar da ita amma sai tayi nasarar watsa musu ‘kasa a idanun su, hakan yasa suka daina gani, ita kuma Mariya ta gudu shima Abdullahi yabi bayan ta rike da robar ruwan da ya debo mata. Bayan Abdullahi ya kawowa Mariya ruwa tasha sai ta fadi ‘kasa ta suma a sanadiyyar jigatar da tayi da kuma raunin da taji a goshin ta. Kafin faruwar hakan a baya Mariya suna soyayya da Abdullahi duk da Yawale ma yana son ta, domin akwai lokacin da ya taba tsayar da ita yana mata magana amma sai tayi masa rashin kunya wanda hakan yasa Abokin Yawale ya mareta amma sai Yawale ya rama mata duk da tayi fushi ta bar musu wajen.

A gefe daya kuma mahaifin Yawale ma yana son Mariya wanda ya kasance Sarkin Fawa a garin (Abdu Kano) Sarkin Fawa mutum ne mai auri saki domin bai yarda a haihu a gidan sa ba, uwargidan sa Talatu (Hadiza Muhammad) itace kadai wadda baya sakin ta domin ita ke kula da gidan sa. Wata rana Sarkin Fawa suna tafe da Tanimu (Musa Mai Sana’a) sai yaga Mariya yaji yana son ta, nan fa Tanimu ya ‘karfafa masa guiwa kuma yaje wajen Habiba mahaifiyar Mariya (Ladidi Fagge) ya sanar mata da cewar Sarkin Fawa yana son auren Mariya amma sai Habiba ta nuna sam bata amince da hakan ba. Haka sai Tanimu ya sake dawowa ya kawowa Habiba kudi don ta amince a aurawa Mariya Sarkin Fawa amma sam ta’ki karbar kudin sa. Hakan yasa Sarkin Fawa da Tanimu suka nufi wajen ‘kanin mahaifin Mariya wato Kawu Bala (Alasan Kwalle) wanda ya kasance me son abin duniya. Jin bukatar su Sarkin Fawa da kuma kudin da suka basa sai ya amince zai bashi auren Mariya amma bayan yaje wajen Habiba da maganar sai ta’ki amincewa. Cikin lokaci kadan Kawu Bala ya karbi kudin auren Mariya da sadaki a wajen Sarkin Fawa sannan yaje ya bawa Habiba wasu daga cikin kudin, amma sam ta’ki karba, saidai hakan bai sauyawa Kawu Bala ‘kudirin sa na aurar da Mariya ba.

Lokacin da Mariya ta samu labarin abinda ke shirin faruwa na auren dolen da za’a yi mata sai ta garzaya taje ta fadawa saurayin ta Abdullahi, nan fa duk hankalin su ya tashi suka rasa mafita har zuwa lokacin da aka daura auren Mariya da Sarkin Fawa.
Bayan auren ne Mariya ta kulle kanta a cikin daki ta’ki amince wa da Sarkin Fawa, duk da irin dabarar da yayi don ta amince dashi amma hakan ya faskara. Shi kuwa Yawale ganin Mariya ta auri mahaifin sa sai ya tsaneta ko kallon arziki ya daina shiga tsakanin su. Wata rana Mariya tana zaune a cikin dakin ta tana sauraron rediyo sai taji ana bada labarin wata mata wadda ta zubawa mijinta guba a cikin abinci yaci ya mutu a sakamakon matar bata son sa. Jin hakan ne yasa Mariya ta fito ta aiki Auwalu dan Sarkin Fawa ta bashi kudi ya siyo mata shinkafar bera ta nuna masa beraye ne suka dameta zata zuba musu magani. A bangaren Abdullahi kuwa ya shiga damuwa saboda rashin samun damar auren Mariya iyayen sa sun rarrashe sa amma sai ya roke su akan su bashi dama ya tafi birni wajen kawun sa. Wata rana Talatu uwar gidan Sarkin Fawa ta bawa Mariya girkin abincin gidan da nufin lokacin karbar girkin ta yayi. Bayan Mariya ta girka abinci sai ta zuba masa shinkafar bera a cikin abincin, har tayi nufin kai wa Sarkin Fawa abinci sai tayi wani tunani wanda hakan yasa ta sauya ra’ayi ta fasa zuba masa guba a cikin abinci, har ta juya zata mayar da abincin sai Talatu ta nufo wajen ta ta nuna lallai sai Mariya ta kai wa Sarkin Fawa abincin yaci domin taga lokacin da Mariya ta zuba gubar, haka Mariya ta kai abincin ba don ranta yaso ba. Ai kuwa bayan su Sarkin Fawa da Tanimu sun ci abincin sai duk suka mutu. Daga lokacin da su Sarkin Fawa suka mutu sai aka mi’ka Mariya ga jami’an tsaro, daga nan kuma aka mika ta ga kotu aka fara shari’a. A wannan lokacin ne wata lauya (Jamila Nagudu) ta roki mijinta (Ali Nuhu) akan ya bata damar tsayawa Mariya a kotu domin ta tausaya mata. Bayan ya bata dama ne aka cigaba da shari’a, yayin da Abdullahi tun kafin hakan ta faru ya soma yawo a wajen lauyoyi irin su (Baballe Hayatu) yana neman lauyan da zai tsayawa Mariya amma sai suka fada masa wasu miliyoyin kudi da zai bayar wanda sam bashi dasu. Daga ‘karshe dai lauyar da ta tsayawa Mariya ta shiga ta fita har aka kori ‘karar su Mariya domin bata kai matakin da za’a yanke mata hukunci ba. Saidai kafin kotu ta kori ‘karar sai lauyar ta kira Talatu kuma ta soma yi mata tambayoyi irin nasu na ‘kwararrun likitoci wanda a sannan ne aka gane cewa Talatu ce ta kashe Sarkin Fawa ba Mariya ba. Nan dai aka yankewa Talatu uwargidan Sarkin Fawa hukuncin kisa, yayin da kotu ta wanke Mariya daga zargin da ake mata.

Bayan dawowar su ‘kauye ne jami’an tsaro suka kama Yawale da tawagar sa saboda yunkurin da suka yi na kashe Mariya. Yayin da Mariya ta cigaba da soyayya da Abdullahi.

Abubuwan Birgewa

1- Marubutan fim din sun yi ‘ko’kari wajen gina labarin, kuma fim din ya tafi kai tsaye domin har ya dire labarin bai karye ba.

2- Anyi ‘kokari wajen samar da kayan aiki masu kyau, kamar su camera da abin daukar sauti, haka kuma an samar da wuraren da suka dace da labarin.

3- Daraktan fim din yayi ‘ko’kari wajen gina fim din ta hanyar da ta dace, haka kuma jaruman sun yi ‘ko’kari musamman Mariya da Yawale.

4- Wa’ko’kin fim din sun nishadantar, haka kuma wasu daga cikin jaruman sun nishadantar da mai kallo, irin su Abdu Kano (Sarkin Fawa) da Tanimu (Musa Mai Sana’a)

Kurakurai:

1- A cikin kotu lokacin da alkali yace ya janye shari’ar Mariya (Maryam Yahya) akan cewar an yi mata afuwa kuma kotu ta wanke ta, ya dace ace an ga matsanancin farin ciki a fuskar Abdullahi (Umar M Sharif) amma fuskar sa a murtuke babu alamar murna duk da irin son da aka nuna yana yi mata.

2- Jarumin fim din Abdullahi ba shi da abinda ake cewar “action” a turance ma’ana kazar-kazar a aikace, sanyin sa yayi yawa domin akwai abubuwan da ya dace ya nuna zafin sa akan su saboda son da yake yiwa Mariya amma bai yiba.

3- An ga Kawu Bala ya fadi ‘kasa bayan sun gama rigima da mahaifiyar Mariya, shin mutuwa yayi ko suma? Sannan kuma menene sanadin hakan? Domin shine wanda bashi da gaskiya kuma shine yaci zarafin ta balantana ace sanadin abinda tayi masa ne yasa zuciyar sa ta buga, shin hakki ne ya kama shi ko me? Ya kamata a wayar da kan me kallo.

4- Wakokin fim din sun yi barkatai, domin da yawa daga cikin su basu sami muhalli ba kawai sako su aka yi.

5- A kotu an ga su Yawale suna hauragiya duk da tsari da doka irin ta kotu amma ba’a ga an tsawatar musu ba, ya dace a nuna musu cewar kotu fa ba ‘kauye bace ballantana suyi abinda suka ga dama a kyale su.

6- Kauyen da suke ciki mai suna kukan ka banza an nuna ‘kauye ne ‘kayau amma wayewar mutanen garin da lafuzan su sam babu ‘kauyanci a ciki, hakan yafi kama da wadanda suke cikin tsakiyar birni.

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma ya samu kyakykyawan aiki daga wajen kwararrun ma’aikata, amma ya yi matukar kamanceceniya da wasu labaran fitattun finafinan Hausa da a ka taba yi a baya-bayan nan, wato Bilkisu Mai Gadon Zinare da kuma Rayuwa Bayan Mutuwa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user