Wednesday 22 August 2018

KARANTA SABABBIN SAKONNIN SOYAYYA NA BARKA DA SALLAH

Tura Wannan Zuwa
FATAN ZAN SAMU ABUN DA NAKE NEMA?


A koda yaushe ina fatan nasara ta kasance a tare da ke, na kasance mai yin fatan kasancewar farin ciki a cikin zuciyar ki a safiya ko rana, amma shin zaki iya tinawa da wani abu wanda zuciyata ke muradin samu daga gare ki? Ba komai bane face ki mallaka min zuciyar ki ta hanyar sanya ni a cikinta ni kadai ba tare da kin hada ni da kowa ba. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.

HADUWAR MU TA FARKO.

Tun daren jiya da na dawo gida nake ta faman sak’a tinani ta yadda aka yi wata ta sace mini zuciyata, to amma dama hakan shi ne burina. Faruwar hakan sai ya zamto tamkar wani al’amarin mafarki ne a gare ni to amma a duk lokacin da na nutsu na zurfafa a tinani ina ji a cikin zuciyata watarana zata zamo mallakina, kin kuwa san wace ce wannan hmm! To ba kowa bace face ke zumar zuciyata, farin cikin raina. A yau sallah nake son na bayyana miki cewa ina son ki.
BARKA DA SALLAH.

KI DAURE KI AMSA KIRANA.

Na shiga damuwa a lokacin da kika nesanta da ni, ki taimaka ki dawo gare ni tun kafin zuciyata ta kara afkawa cikin hali na damuwa, yau ranar farin ciki ce a gare ni da dukkan sauran musulmin duniya gimbiyata a saboda haka nake kara jaddada miki cewa, ina kaunar ki.
BARKA DA SALLAH.

SAKE-SAKEN ZUCI.

A cikin dukkan mafarkan da nake yi bayan haduwata da ke, ban taba ganin wata rana da ta zo ta kuma wuce ba tare da na gambu tare a cikin lambu mai sanyaya zuciyar masoya ba, rayuwa ce mai dadi ke gudana a tsakanin mu, ina fatan wannan rana ta bayyana a gare ni a zahiri ba a cikin mafarki ba kawai. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.

KI RIKE ALKAWARINA.

Salimat, ina son ki san cewa shi so da kike gani tamkar tab’o ne, adadin yadda ka yi tsalle ka fad’a a cikin shi tofa adadin hakane zai baka wahala a lokacin da ka tashi fitowa, ina fatan mu rik’e juna da amana har abada. Ina fatan dorewar farin cikin ki.
BARKA DA SALLAH.

SARAUNIYAR BIRNIN MASOYA.

A duk lokacin da na zauna ina yin nazari a dangane da soyayyar mu, sai na hasashen cewa dama a ce fikafikai za su bayyana a jikina da na nausa da ke izuwa kayatacciyar fadar dake can babban birnin masoya na sabuwar duniyar mu domin sada ki da kujerar alfarma ta mukamin sarauniyar ‘yan matan duniya da na dade da baki. Shin Rukayya kin kuwa lura da cewa ina neman na zama zautacce a cikin soyayyar ki? Na nitse a cikin son ki ta yadda ba zan iya fita ba. Soyayyar mu ta dabance a cikin wannan duniya ta mu da muke ciki. Soyayyar mu ta zamto tamkar wani rubutaccen labari ne wanda masoya za su shekara suna nazari a kanta. Fatana dai mafarkina ya zamo gaskiya a dangane da ke.

BARKA DA SALLAH.

ZAN ZAMO MIKI GARKUWA.

Alkawari ne na dauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matukar muna a tare da juna, ina fatan nan da wani dan lokaci ki tabbatar da hakan bayan kin zamo mata a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa Fatima, ki huta lafiya. Ki kula min da kanki. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.

KINA DA KYAU MASOYIYATA.

Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne? Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske? Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wadda ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni d’aya cikin kad’aici a dare ko safiya. Ke ce abar so na.
BARKA DA SALLAH.

ZAN BAYYANA MAKA SIRRINA.

Amincin Allah ya tabbata a gare ka sahibina, a yau ne nake son na kara bayyana maka matsayin ka a gare ni, tabbas Abba ka zamo wani jigo na dorewar farin ciki a zuciyata. Fuskar ka ce abun da nake kallo na samu farin ciki cikin gaggawa. Karda ka damu ‘Dan-Hausa da rashin bayyana maka gaskiyar al’amari amma a yau ranar sallah kuma ranar farin ciki da murna nake son furta maka cewa ina son ka! Ina son ka!! Ina son ka Abba!!! Daga masoyiyarka Rukayya.
BARKA DA SALLAH.

DAMA A CE HAKAN YA KASANCE A ZAHIRI.

A kullum na kan yi mafarkin ga mu a tare cikin d’aki tare da ‘ya’yan mu, shin ko hakan yana nufin za mu mallaki juna kenan? Tabbas idan hakan ya kasance bani da wani sauran buri a rayuwata face na yi fatan kasancewa a tare da kai a gidan aljanna. Ina son ka, ka kula min da kanka karda ka bari kowace kazamar yarinya ta rabe ka. Ni ce taka Mardiya.

Karanta Sababbin Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zukatan Ma'aurata Domin Ma'aurata Maza da Mata

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user