Tuesday 21 August 2018

KARANTA CIKAKKEN JAWABIN SHUGABA MUHAMMADU BUHARI GA 'YAN NIJERIYA JAWABI MAI RATSA ZUCIYOYI - HOTUNA DA CIKAKKEN JAWABI

Tura Wannan Zuwa Ga
Ya ku 'yan uwana 'yan Nijeriya.

Muhammadu Buhari

Marubuci: Bashir Ahmad

1. Ina mai matukar godiya ga Allah da kuma daukacin 'yan Nijeriya saboda addu'o'in da suka yi mini. Ina farin cikin dawowa gida cikin 'yan uwana maza da mata.

2. Yayin da nake jinya a kasar Ingila, ina samun labaran abubuwan da ke faruwa a gida.

3. 'Yan Nijeriya suna tattauna al'amuran da suke faruwa, amma na fahimci cewa wasu daga cikin kalaman da ake yi musamman a kafofin sada zumunta sun ketara iyakar dokokin kasar nan inda suke sanya alamar tambaya game da ci gaba da kasancewarmu a matsayin kasa guda . Wannan wani abu ne na wuce gona da iri.

4. A shekarar 2003 bayan da na shiga siyasa, marigayi Cif Emeka Ojukwu ya taba ziyarta ta kuma ya zauna wurina a Daura.

5. Mun kwashe fiye da kwana biyu muna tattauna matsalolin Najeriya, a wasu lokutan mukan shafe dare muna magana. A karshe mun cimma matsayar cewa wajibi ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya kuma dunkulalliyya.

6. Hadin kan 'yan Nijeriya wani abu ne da aka cimma matsaya a kai. Kuma ba za a taba warware shi ba.

7. Ba za mu bari wasu marasa dattako su fara tada fitina kuma idan abubuwa suka lalace su gudu su bar wasu da aikin dawo da doka da oda, wata kila ma hakan ba zai yiwu ba sai an zub da jini.

8. Kowane dan Nijeriya yana da 'yancin rayuwa da kuma gudanar da harkokinsa a ko ina a Nijeriya ba tare da an yi masa wani shamaki ba.

9. Na yi amannar cewa dimbin 'yan Nijeriya suna da irin wannan tunani.

10. Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kwararan batutuwan da suke damunmu.

11. Kowane bangare yana da korafinsa. Amma dadin tsarin da ake tafiyar da kasar a kai yanzu shi ne, yadda ya ta nadin hanyoyin da duk wadanda suke ganin an yi musu ba daidai ba, za su iya gabatar da korafinsu da kuma yadda za a ci gaba da tafiya tare.

12. Majalisar dokoki ta kasa da kuma majalisar koli ta kasa su ne wuraren da doka ta yarda a tattauna manyan batutuwan da suka shafi Nijeriya.

13. Baki ya zo daya a kasa baki daya cewa ya fi kamata a ci gaba da zama tare maimakon a raba kasar.

14. Bugu da kari, ina kira da rundunonin tsaro da kada nasarar da aka samun a watanni 18 da suka gabata ta sa su, su rage kaimi.

15. Wajibi ne mu yaki 'yan ta'adda da miyagu kuma mu ga bayansu saboda mu ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da tsaro.

16. Wannan ya sa za mu kara kaimi ba kawai a yaki da 'yan Boko Haram ba wadanda suka fito da sabbin hanyoyin kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hari.

17. Hakazalika za mu sa kaimi a yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa da rikicin Fulani makiyaya da manoma da rikicin kabilanci wanda wasu 'yan siyasa masu munanan manufa suke rura wutarsa. Za mu magance su duka.

18. A karshe 'yan uwana 'yan Nijeriya abin da ya dace yanzu shi ne mu manta da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu fuskanci wadannan kalubalen da suka shafe mu duka; wato gyara tattalin arziki da bunkasar siyasa da hadin kan kasa, har ila yau, da samar wa 'yan Nijeriya dawwamanman zaman lafiya.

19. A shirye nake don ganin mun cimma wannan burin da kuma ganin d o rewarsu. Ina farin cikin dawowa gida.
20. Na gode kuma Allah Ya albarkaci kasarmu.

Kwalliyar Sallah a garin Daura

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai hakura da yaki da cin hanci da rashawa ba duk da ya janyo ma sa kiyayya da bakin jini ga wasu.

A cikin sakonsa na sallah ga al'ummar Najeriya mai dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban na musamman kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban na Najeriya ya bukaci dukkanin musulmi su yi amfani da wannan damar domin yi nazari da yin karatun ta-natsu tare da kasancewa jekadu nagari ga addininsu ta hanyar yin aiki da koyarwarsa.

Buhari ya kuma bayyana cewa adddini wani abu muhimmi ne da ke tasiri ga halayen mutum da kuma ayyukansa.
A cikin sakon na Sallah, shugaban ya kuma bayyana damuwa da nadama kan yadda ya ce, son kai da hadama da cin hanci da rashawa ya sa wasu sun yi watsi da imaninsu domin cimma burinsu na rayuwa.

"Mika wuya ga yaki da rashawa ba zabi ba ne domin yana lalata al'umma da ci gaban kasa."

A cewar shugaban, " ko da kuwa yaki da rashawa ya janyo maka bakin jinni ga wasu, ba zai sa ka kariya ba a matsayinka na shugaba domin yin hakan tamkar cin amana ne ga jama'a."

Shugaban ya bukaci 'yan Najeriya su rungumi hanyoyi na tabbatar da zaman lafiya da hakuri da juna a kowane lokaci ta hanyar kawar da son zuciya da duk wasu bukatu na akidu ko kuma kungiyoyi.

KARANTA YANZU KAJI: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA AL'UMMAR AREWACIN KASAR NIGERIA - WASIKAR TA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI


Ɗaukacin Ma'aikatan wannan Shafi Mai Albarka na taya Al'ummar Musulmi Barka da Sallah dafatan Allah ya Amshi Ibadun Mu.

Muna fatan za'ayi shagulgulan Sallah Lafiya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Muryar Hausa24 and Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user