Saturday 18 August 2018

Kofi Annan ya kwanta dama - Karanta Abubuwan da baku sani ba dangane da Rayuwar Kofi Annan

Tura Wannan Zuwa Ga
Tsohon sakataren janar na Majalisar Dinkin Duniya,Kofi Annan ya kwanta dama a asibitin birnin Bern na kasar Switzerland,inda ake jinyar sa.


Kofi wanda ya zama sakataren majalisar Dinkin na bakwai a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1996, ya yi wafati bayan ya share shekaru 79 a duniya.

An haifi Annan a birnin Kumasi da ke gabashin kasar Ghana a ranar 8 ga watan Afrilun shekarar 1938.

Annan ne bakar fata na farko da ya zama shugaban majalisar ta dinkin duniya, inda ya yi wa'adi biyu tsakanin shekarun 1997 da 2006.

Daga bisani ya zama wakilin majalisar dinkin duniya na musamman a Syria, inda ya jagoranci yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Marigayin ya shugabanci majaliar dinkin duniya ne a daidai lokacin da aka soma yakin Iraki da kuma barkewar annobar cutar HIV/Aids.

Mr Kofi Annan ya taba lashe kyautar lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya a 2001.

Kofi Annan ya bayyana cewa babbar nasarar da ya yi a duniya ita ce ta samar da shirin nan na Ci gaban Muradun Karni - wanda ke da zummar rage talauci da mutuwar kananan yara.

Sai dai ya sha suka a wasu bangarori. Masu sukar tasa sun caccake shi saboda gazawar majalisar dinkin duniya wurin tsayar da kashe-kashe kare-dangi a Rwanda a shekarun 1990 lokacin da yake shugabantar hukumar tabbatar da zaman lafiya ta majalisar.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Trt Hausa and Bbc Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user