Wednesday 17 October 2018

Karanta Kaji: Dalilin Da Yasa Nakeson Aure a halin Yanzu da kuma Irin Mijin danake son Aura - Hafsat Idris Ɓarauniya

Tura Wannan Zuwa Ga
A farfajiyar finafinan Hausa wato Kannywood mutane da yawa suna ganin ‘Yarwasa Hafsat Idris a matsayin sabuwar ‘yarwasa amma kuma ita jaruma ce domin tun da ta fito a wata fim mai suna Barauniya ta zama babbar Jaruma saboda hazakar da ta nuna a fim din.Gidan jarida ta yi hira da Hafsat Idris yayin da take daukar wata sabuwar fim mai suna ‘Gimbiya Sailuba’ a garin Abuja.

Da aka tambayeta akan daukakar da ta samu na faraddaya a harkar fim, Hafsat tace “Ikon Allah ne kawai da kuma himma da na sa akan sana’ar saboda ban taba irin wanan aikin ba amma tun da ta fara fitowa a fina-finan Hausa gaba na ke ta yi kuma ina wa Allah godiya da kuma kamfanin Maikwai Records da ta fara saka ni a fim.

Ta kuma ce za ta so ta cigaba da aikin fina-finan Hausa duk da cewa aure ne ke gaban ta a yanzu haka.

“Kwarai da gaske ina da saurayin da na ke matukar so sai dai ba dan fim bane.”

Bayan haka kuma Hafsat Idris ta bada bayani akan dangartakarta da Jarumai Nafeesa Abdullahi da Rahama Sadau da kuma a me zata fito a wasan ‘Gimbiya Sailuba’’

” Dangartakana da Rahama da Nafeesa ba ya wuce a wurin aiki. Idan aiki ya had mu zamuyi tare cikin fara’a da nishadi amma bayan haka babu wata alakar kawance da ke tsakani na da su.

A cikin Fim din Gimbiya Sailuba kuma, Hafsat tace za ta fito ne a matsayin gimbiya, san kowa kin wanda ya rasa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Premium Times Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user