Wednesday 17 October 2018

Karanta Kaji: Saudiyya ta Bayar da Taimakon Dala Miliyan 100 ga 'yan ta'adda a Arewacin Siriya

Tura Wannan Zuwa Ga
Masarautar Saudiyya ta sake bayar da miliyan 100 ga Amurka don amfanin 'yan ta'addar aware na YPG/PKK da ke arewacin Siriya wadanda suka mamayi yankunan da suke.



Jaridar New York Times ta rawaito cewa, ta bayar da labarin cewa, gwamnatin Saudiyya da ta shiga mawuyacin hali saboda batan dan jaridar Jamal Kashoggi ta bayar da kudin ga Amurka a lokacin da Ministan harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ke ziyara a Rasha.

Amurka ta dade tana neman wannan kudi amma yadda Saudiyya ta biya a lokacinda Pompeo ke yawon ziyara game da batan dan jaridar Jamal Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a ranar 2 ga Oktoba, na da jan hankali sosai.

Jaridar ta New York Times ta rawaito wani na cewa, wannan abu ba wai arashi ba ne kan yadda Amurka ke kallon manufofinta a Siriya.

Jaridar ta rawaito bayanin da mai ba wa Trump shawara kan yaki da Daesh Brett McGurk ya yi.

McGurk ya musanta cewa, biyan kudin na da alaka da ziyarar da Pompeo ke yi.
McGurk ya kare cewar tun watan Agusta Saudiyya ta yi alkawarin bayar da kudin kuma a watannin bzara aka sarna za a biya.

A watan Oktoban 2917 Ministan kasa na Saudiyya Samir Al-Sabhan ya ziyarci yankin Ayn ısa da ke rakka wanda 'yan ta'addar awaren na YPG/PKK suka mamaye.
Bayan wannan ziyara ne Saudiyya ta bayar da taimakon dala miliyan 100 don gyara gine-ginen da Amurka, YPG da PKKsuka rsa a lokacin da suka ce suna yaki da 'yan ta'addar Daesh.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: TRT HAUSA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user