Friday 19 October 2018

KARANTA KAJI: WA YA ƊANAWA GANDUJE TARKO ?

Tura Wannan Zuwa Ga
Labari ya karade 'kasa, kafofin watsa laburu sun yi ca, Duniya kuma duk ta daukwa ana ta yamididi da zargin gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, Khadimul Islam ya karbe Dalar rashawa da cin hanci ya danna cikin aljihu da takardu cikin wasu faya-fayan bidiyo da aka yada.


Marubuci: Garba Tela Hadejia

Har zuwa yau, labarin na cigaba da karada Duniya, kuma al'umma daban-daban su na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu mabambanta kan wannan al'amari, wasu na gaskata fayafayan bidiyon wasu kuwa na daukwarsa a matsayin sharri da 'kage domin a 'batawa gwamna Ganduje suna.
Sai dai kuma, a 'bangarenta, gwamnatin Jihar Kanon, ta ci alwahin shigar da 'kara Kotu kan zargin 'bata suna da da ta ke yi wa gidan jaridar na (Daily Nigerian) karkashim jagorancin mawallafin jaridar, Malam Jafar ja'afar.

Shi kuma a nasa 'bangaren, Jafar Jafar, ya kafe 'kyam ya yi tsayuwar daka cikin 'karfin gwiwar yarda da sahihancin labarinsa tun ma kafin ya yada.

Ita kuma majalissar dokokin Jihar Kano, har ta yi azamar kafa kwamitin bincike domin nemo gaskiyar al'amari.

A gefe guda kuwa wasu daga cikin jami'ai da hadiman gwamnatin Kano, gami da wasu daga cikin masu sana'ar shirya fina-finai suna cigaba da ba wa gwamna Ganduje kariya.

A dan nazarin da na yi kan wannan batu, ko shakka babu wannan al'amari a iya cewa zai zame wani gagarumin 'kalubale ko wata gagarumar sarkakiya ko tsaka mai wuya ga wasu 'bangarori kamar haka:

1. Idan har ta tabbata wannan faifan bidiyo kirkirarsa aka yi, to ba shakka, an 'batawa gwamna Gwanduje suna kuma kamfanin jaridar zai iya fuskantar hukunci biyan tara ladan 'bata suna. Kuma daraja da kimar mawallafin da na gidan Jaridar ya zuba a idon Duniya. Kana jama'a za su daina gamsuwa da sahihancin labarinsu.

2. In ko ta tabbata gaske ne, to ba makawa kallo zai iya komawa sama, mutane za su maida hankali kacocan kan fadar shugaban 'kasa (Alhaji Muhammadu Buhari) mai rajin yaki da rashawa gami da jam'iyyar (APC) mai ikirarin kawo sauyi domin ji da ganin irin matakin da za su daukwa akai.

Idan ko suka nuna halin ko'inkula, ko suka 'dauki mataki na sako-sako, to daraja da kimar gwamnati kan yaki da rashawa za su ragu a idon al'umma da ma Duniya. In kuwa suka dauki matakin azo a gani to ba shakka martaba da kimar gwamnatin za ta sake 'karuwa, sannan 'yan 'kasa da Duniya gaba 'daya za su sake samun nutsuwa da yarda da ikirarin da gwamnatin take yi kan yaki da cin hanci da rashawa ba sani ba sabo.

3. Sannan idan har ta tabbata gaskiyar kuma hukunci mai tsanani ya biyo ta kan gwamna Ganduje, to ba shakka, za a iya danganta wannan al'amari da "rana dubu ta 'barawo, daya tak ta me kaya". Ma'ana ya jima yana karba rana daya ta fashe. Ko kuma a iya cewa "Gadar Zare Gwamna Ganduje ya taka", ko kuma wani danannen tarko aka dana masa ya bi ta kai. Ma'ana wadanda suka shirya al'amarin ba da na goron tare da nadar faifan bidiyon sun san yana da halin cin hanci da rashawar, ko kuma ba halinsa ba ne amma sun rude shi da daloli ya fada, su a karan kansu ko wasu makiya Gandujen ne suka hada baki da su wajen shirya masa wannan gada, kan wata manufa tasu ta daban ko kuma da nufin su yi amfani da ita a daidai wannan lokaci na kakar zabe, shi kuma ya taka, take kuma neman yin tafiyar ruwa da shi.

Abin jira a gani dai shi ne, samun sahihin bayanai kan ingancin faifan bidiyon daga masana kuma kwararru a fannin gami da binciken majalissa da na sassan tsaro, da kuma irin wainar da za a toya idan an kara a kotu da kuma bayan bayyanar sahihanci ko akasin haka na faifan bidiyon.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user