Tuesday 19 March 2019

KARANTA KAJI: KALUBALEN DAKE GABAN GANDUJE IDAN YACI ZABE A KARO NA BIYU

Tura Wannan Zuwa
Duk da cewar za6en har yanzu bai kammala ba.

Ganduje


Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Amma a bisa kididdigar da take hannu, ta nuna cewa Abba da Ganduje ne a kan gaba, inda a jiya nayi dan takaitaccen bayani akan wasu daga cikin kalubalen da Abban zai iya fuskanta idan ya samu darewa kujerar gwamnan jihar Kanon, yau kuma zan kawo wasu daga cikin kalubalen da Gandujen ka iya fuskanta idan ya samu tsallakewa.


Duk da cewar Gandujen ne akan kujerar gwamnan jihara Kano kusan shekaru hudu da suka gabata, amma i zuwa yanzu za'a iya cewa matukar ya koma kujerar gwamnan to zai iya fuskankantar wasu tarin kalubale, wasu daga cikinsu sun hada da:

1. Shari'a.
Ba lalle ne idan ya samu tsallakewa 'yan adawa daga sauran jam'iyyu, musamman ma PDP su kyaleshi ba, dan kuwa zasu garzaya kotu ne neman hakkinsu, tare da rokon kotun da ta kar6e za6en ta basu, ko kuma ta umarci hukumar za6e da ta koma ta shirya wani sabon za6en, kamar yadda ta ta6a faruwa a wasu jahohi irinsu Osun, Ekiti da sauransu.

Hakan ce zata d'aid'aita gwamnatin, koyaushe tana hanyar kotu, inda za'a kare iya wa'adin da zaiyi akan mulkin ba tare da an tsinana komai ba.

2. Rabon Muk'amai.
Kasancewar dukkanin wasu jiga-jigan 'yan siyasa dake jihar ta Kano a halin yanzu sun koma jikin Gandujen, hakan ce zata saka gabaki daya lamuran gwamnatin zasu dagule, domin kuwa kowa zai saka rai ne da cewa za'a bashi wata kujera, inda da zarar rabo yayi nisa wani yaga bai samu ba, to anan zai fara tada rigima, tare da tone-tone da kuma fadar maganganu, wanda idan ba'ayi wasa ba, gwamnatin ka iya darewa gida-gida, har a samu 'yan adawar cikin gida.

3. Majalisar dokokin jihar Kano.
Duk da cewa izuwa yanzu za6a66un 'yan majalisar dokokin jihar Kano na jam'iyar adawa ta PDP basu wuce daya bisa uku ba (1/3), amma matukar suka kasance wayyayu, kuma jajirtattu to zasu iya hada kai a majalisar, ta inda zasu zamewa 'yan majalisar gwamnati ala kakai, tare da yin fatali da dukkanin wani abu da gwamnan zai nema daga garesu, wanda idan ba'a yi wasa ba ma, zasu iya jan hankalin wasu daga cikin 'yan APC din, su 6ullo da hanyar da zasu samu fita daga jam'iyar, ko kuma subi matakin shari'a a kar6e kujerun.

4. Ware masoyansa na gaskiya.
Kasancewar gwamnatin ta Ganduje ta tara mutane da dama kama daga tsofaffin gwamnoni guda 2, tsofaffin mataimakan gwamnoni guda 2, tsofaffin sanatoci wajen guda 5, kwamishinoni na da dana yanzu, tsofaffin ministoci, 'yan majalisar wakilai ta tarayya da majalisar dokoki ta jiha na da dana yanzu, shugabannin kananan hukumomi da kansiloli na da dana yanzu, da sauransu.

Amma kuma ace ana wasan kura da gwamnatin a filin za6e kamar haka, kasan kuwa akwai sa hannun wasu daga cikinsu, saboda haka sannan ne zai gane masu taimakonsa da kuma masu taimakon aljihunsa, ya rike masu taimakon nasa da hannu bibiyu.

5. Matsin lamba daga jama'ar gari.
Ba lalle ne jama'ar jihar Kano suci gaba da yi masa uzuri ba a sabgar gudanar da gwamnatin, ta inda zai ringa shan kushe akan dukkanin wasu ayyuka da zai kawo, komai muhimmancinsu kuwa, wanda idan ba'a yi wasa ba a lamuran da dama mutane ka iya fitowa zanga-zanga, ko kuma su ringa yiwa jami'an gwamnatin ihu, dan kuwa ba lalle ne su ringa bibiyar lamuranta ba.

6. Gina gidansa na siyasa.
Har kawo yanzu idan ana maganar siyasar Kano, ba zaka ji wani mutum guda da za'a ce maka daga gidan Ganduje ya fito ba, dan kuwa har yanzu bashi da yara a siyasance, sai dai yara a gwamnatance.

Saboda haka matukar yana so siyasarsa ta dore, to wajibi ne ya gina mutane, musamman ma matasa da zasu iya tashi da akidarsa, kamar yadda Kwankwaso ya gina nasa, sannan kuma ya iya ware masoyansa na hakika daga cikin masu son abin hannunsa, domin koda a nan Social Media zaka ga cewar bashi da tsayayyun masu kare gwamnatinsa da kuma tallata ta kamar yadda Buhari da Kwankwaso suke dasu.

Wadannan sune wasu daga cikin kalubalen da Gandujen ka iya fuskanta, wanda idan hali yayi, nan gaba zan iya karo wasu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Source: www.MuryarHausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user