Wednesday 20 March 2019

KARANTA KAJI: KALUBALEN DAKE GABAN ABBA KABIR YUSUF IDAN YACI ZABE

Tura Wannan Zuwa Ga
KALUBALEN DAKE GABAN ABBA K YUSUF IDAN YACI ZABE.

Abba Kabir Yusuf

Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Tun bayan da aka gudanar da za6en gwamnan jihar Kano, wanda hukumar za6e ta kasa ta bayyana cewa bai kammala ba, sakamakon wasu 'yan kura-kurai da matsaloli da aka samu nan da can, mutane da dama ke ta bayyana ra'ayinsu akan za6en wanda yake nuna cewa i zuwa yanzu dan takarar jam'iyar PDP Abba Kabir Yusuf ne ke kan gaba, da kuri'u kimanin miliyan daya da 'yan kai, sai dai an zuba ido aga yadda zata kaya zuwa ranar da za'a dawo a kammalashi, wanda zata iya yiwuwa ya samu nasara, zata iya yiwuwa kuma a samu akasin hakan.

Sai dai kuma, sakamakon wani dogon bincike da nayi, na gano cewar, matukar Abban yayi nasara, to kuwa zai gamuwa da wasu tarin kalubale, wasu daga cikinsu kuwa sun hada da:

1. Majalisar Dokokin jihar Kano.
A sakamakon za6en da hukumar za6e ta bayyana izuwa yanzu, ya nuna cewar, jam'iyar APC ce take da rinjaye a majalisar dokokin ta jihar Kano, yayin da jam'iyar PDP kuma ke da kujeru kimanin 1 bisa uku (1/3) cikin kujeru 40 dake majalisar.

Wanda hakan ba karamin kalubale bane gareshi, dan kuwa da wuya 'yan majalisar su yarda a za6i shugaban majalisa (Speaker) da kuma sauran manyan kujerun shugabancin majalisar daga tsagin jam'iyar PDP, haka nan dukkanin wani kuduri da gwamnan zai aikewa majalisar zai dade yana watangaririya kafin ya samu sahalewar biyu bisa uku na 'yan majalisar, inda za'a saka siyasa da banbancin jam'iya a gaba, ayyukan da zasu kawowa jama'ar jihar Kano ci gaba, sannan kuma zasu dinga kar6ar umarni ne daga jam'iyarsu ta APC.
Akwai yiwuwar 'yan majalisar su zame masa ala kakai, su ringa saka masa ciwon kai, kamar yadda su Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka zamewa Shugaba Buhari a majalisa ta 8.

Matukar gwamnan yana son cimma muradinsa, to ya zama lalle ya nemi hanyar da zata fishsheshi.

2. Asusun gwamnatin jihar Kano.
Ba lalle bane ya tarar da wani abin kuzo mu gani ba cikin asusun jihar Kano daga gwamnatin da zai gada, dan kuwa idan baiyi wasa ba ma zai iya tarar da dimbin bashi a ciki, wanda gwamnatin zata dade bata iya biya ba, ballantana kuma har ta samu aiwatar da wani abu cikin gaggawa daga hawanta, kamar yadda al'ummar jihar ta Kano suke tsammani daga gareshi.

3. Haraji.
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiri hukumar kar6ar haraji ta jihar Kano (Internal Revenue) inda ake kar6ar haraji daga hannun al'umma daban-daban a cikin jihar, wanda har ta dauki ma'aikata, ta bude musu ofisoshi daban-daban a sassan jihar.

Abin dubawar a nan shine:

Shin idan Abban yayi nasarar kar6ar mulkin zai ci gaba da aiki dasu ne ta hanyar kar6ar harajin shima?

Idan kuwa ba zai ci gaba da aiki dasu ba, hakan na nufin zai koresu ne daga aikin ko kuma wata ma'aikatar zai canza musu?

4. 'Yan kasuwa.
Kasuwanni da dama dake birnin jihar a yanzu an matsesu, ta hanyar yanka sababbin shaguna, wanda ya haddasa karin cinkosu a cikin kasuwannin, inda har takai ana iya yanka gaban runfar mutum a siyarwa da wani, wanda har sai da takai an yanka babban masallacin Idi na tsakiyar birnin Kano tare da wani 6angare na Stadium din Kofar Mata, an siyar dashi ga wasu 'yan kasuwa dan su gina sababbin shaguna.

Shin idan Abban yayi nasara gwamnatinsa zata kyale wadancan wurare ko kuwa zata kar6esu ne?

Idan zata ka6esu to menene makomar wadanda suka siya, za'a biyasu diyya ne ko kuma a'a?

5. Kwamishinoni.
Kasancewar dukkanin wadanda suka yi kaurin suna a 6angaren tafiyar Kwankwasiyya sun koma 6angaren Ganduje, wanda hakan ke nuni da cewar saura fitattun mutane 'yan kadan ne suka rage a tsagin Kwankwasiyyar, wadda idan har Allah ya bawa Abban nasara to kuwa za a ga sababbin yankan rake a kujerun Kwamishinoni masu bawa gwamna shawara da mataimaka na musamman, wanda hakan ke nuni da cewar, Abba da Kwankwaso ne zasu zage damtse wajen dora wadancan mutane a hanya, tare da kokarin koya musu yadda zasu gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da gwamnatin ta fuskanci matsala ba.

6. Matasa.
Kusan za'a iya cewa matasa sun taka muhimmiyar rawa wajen zazzagawa Abban ruwan kuri'u, wanda ba dan su ba za'a iya cewa da yanzu Abban bai samu adadin kuri'un da ya samu ba.

Yanzu haka dai irin wadancan matasa da suka tamakawa Abban wajen samun kuri'u zasu baza ido ne idan gwamnatin ta samu nasara, tare da sa ran cewa kowanne daga cikinsu sai ya amfani gwamnatin.

Wajibi ne kuma gwamnatin ta 6ullo da wasu hanyoyi da zasu dakile harkar daba a tsakanin matasan jihar, sannan ta fito da hanyoyin da zata rage zaman banza tsakaninsu ta hanyar daukarsu aikin gwamnati da kuma sama musu ayyukan yi da sana'o'i.

7. Jama'ar gari.
Sauran jama'ar gari da dama, musamman ma wadanda suka sayi wasu filaye da Gwamnatin Ganduje ta yanka a tsakiyar Badala da kewayenta suna cikin zullumi akan makomar wuraren da suka siya, dan kuwa ko a Kwanakin baya sai da wata tirka-tirka akan irin wannan badakala takai ga dakatar da shugaban karamar hukumar Dala, domin ayi bincike akan lamarin.

Abin dubawar a nan shine, shin idan Abban yayi nasara zai kyale irin wadancan wurare ne ko kuwa zai kar6esu.

Idan gwamnatin ta kar6e zata biyasu diyya ne ko kuma a'a?

Wadannan kadan kenan daga cikin kalubalen da Abban zai iya fuskanta a tashin farko idan yayi nasarar darewa kujerar gwamnan jihar Kano, akwai wasu da dama jingim, wadanda idan hali ya bayar nan gaba zan dora akansu.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user