Friday 12 April 2019

KARANTA KAJI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA TARA

Tura Wannan Zuwa
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen Hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.






Darasi Na 9

KALMOMIN JAMA’U

Wasu kalmomi ne da ke nuna gamewa ba tare da togaciya ba. Irin waɗannan kalmomi na jama’u su ne: komai, kowa, ko’ina, koyaushe, kowane, kowace, kowanne, kowacce, kowaɗanne.
Yayin rubutu, ana rubuta kalmomin jama’u ne a matsayin kalma guda, ba tare da rabawa ba.

Misali:

kowane gari, ba ko wane gari ba

ko’ina ka je, ba ko ina ka je ba

koyaushe ne, ba ko yaushe ne ba

HUKUNCE-HUKUNCEN “WA”

Harafin “wa” iri biyu ne dangane da yadda akan faɗe shi, haka ma yayin rubutu, kamar haka:

“wa” Jakada

Yakan biyo bayan aikatau (kalmar da ke nuna aiki) ne a cikin jumla, sannan kalmar sunan wanda aka yi aikin domin sa kan biyo bayansa. To shi wannan nau’i na “wa” daban ake rubuta shi, ba a liƙa shi jikin kalmar aikin.

Misali:

sun kamo wa Audu kifi

ta dafa wa baƙi abinci

ya ɗora wa yara laifi

“WA” ƊAFA-ƘEYA

Shi kuma wannan yayin rubutu, ana liƙa shi ne a jikin kalmar aikin, wanda hakan kan sauya masa matsayi daga aikatau zuwa suna, wato sunan aiki ke nan.

Misali:

kamowa suka yi

dafawa ta yi

ɗorawa zai yi.


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah.

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad .

KARANTA KAJI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA TAKWAS


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com

Mungode .



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user