Tuesday 18 June 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 1: LABARIN YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa Ga
A zamanin da cikin kasar Arewa, an yi wani gawurtaccen manomi a Langeri cikin kasar Tanis, ana kiransa Nakowa, abin da ya sa a ke kiransa haka don yawan alherinsa da fara’a ga jama'a har ya zama kamar kowa nasa ne a garin.Tauraruwar Hamada
Marubuci: Bukar Mada
+2348021218337Na Sa'idu Ahmed Daura


Ko da ya ke kasar nan da Nakowa ke zaune tana cikin yankin Saharah amma Allah ya yalwata ta da dausayoyi manya manya kusa da kusa masu albarka, wadanda su ke noman shinkafa da alkama da sauran kayan lambu, wajen dabino ba sai am fada ba. Nakowa ya mallaki dausayoyi masu yawa, ga shi kuma da bayi masu yawa, wadanda akasari shi ne ya ciwo su wajen hari, don fa wajen jaruntaka ba kamarsa duk kasar. To, bayin nan su ke yin duk dawainiyar aikin gonakinsa ko da yake a ko yaushe yana tare da su. Idan suka fita da safe ba su dawowa sai magariba. A takaice dai a zamanin nan a Arewa babu attajiri kamarsa.


Nakowa masoyin malamai ne kwarai da gaske, sabo da haka har ya nemi wani malami suka yi abota. A bisa al'adarsu kullum tare su ke fira da abokinsa malamin nan su cika dare. To, malamin nan abokinsa ma’abucin karatun littafai ne masu ba da labari da hikayoyi.

Wata rana malamin yana karanta wa Nakowa labarin wani kasaitaccen Sarki da aka yi a Kasar Gabas, sai Nakowa ya ce wa malamin, “Ya fi kyau ka karanta mani labarin kasaitaccen attajiri don zai fi mana amfani.” Malami ya ce, “I, ai ko gaskiyarka," sai ya duba littafi ya ce, “To, bissimillah."


‘A cikin kasar Gunzur an yi wani attajiri a Kira kudancin Birnin Gunzur, misali tafiyar yini, ana kiransa Mairabgaja. Ga wannan zamani babu wanda ya kama kafarsa a dukiya, ga shi kuma wajen alheri kamar a ce ya fi kowa. Don tsananin alherinsa kusan kullum Sarkin Gunzur a Kira ya ke yini gun Mairabgaja. Kuma sunansa Lukumanu ba Mairabgaja ba, mutane ne suka yi masa lakabi da haka don irin abincin da yake shiryawa kullum a gidansa don jama‘ar gari da baki, don lalle abincin ya isa jarin yaro.


To duk abin nan da Mairabgaja ya tara na banza ne, kuma abin da ya ke ma jama’a na banza ne don ba shi da magaji, ko bari ba a taba yi masa ba. Yayin da malamin nan ya zo nan, sai ya ga Nakowa yana kuka duk hankalinsa ya tashi. Malami ya nemi kai da kafar Nakowa ya rasa, ba abin da ya ke sai kuka. Saboda haka malamin ya fito ya nufi gidansa ya bar shi cikin wannan hali.


Al'adar malamin ce ba ya zuwa gun Nakowa sai dare ya kusa rabawa amma kashegari tun da almuru ya zo, ya tarad da shi dai ba ya da wani sukuni, hankalinsa in ya yi dubu duk ya tashi. Malami ya tsugunna suka gaisa, sa‘an nan ya dukad da kansa kasa ya ce, ”Ina so ka bayyana mani dalilin bacin zuciyarka na jiya." Nakowa bai amsa ba. Da malamin ya nace masa da tambaya, sa'an nan ya daga kai ya ce, “Ka sani ba ni da da ko diya, ni kuma na tambaye ka ka ba ni labarin wani kasaitaccen attajiri, don in ji irin dubarunsa ko na sami wadanda za su yi mini amfani.“ To, da farawa sai ka soma yi mani habaici, kana cewa, duk 'dukiyar da attajirin nan ya tara, ta banza ce, don ba shi da magaji, watau ni." Da malamin nan ya ji inda Nakowa ya nufa sai fa hankalinsa ya tuma, ya fadi yana rantse-rantse gaban Nakowa, kan shi ko a zuci bai kawo haka ba. Da Nakowa ya ga malami da gaske ya ke, sai ya ce, “To, ai ba komi, ka san zato zunubi ne ko da ya zama gaskiya ne.” Ya nemi gafarar malamin. Ya gafarta masa.


Sa’an nan malamin ya duka ya ce, “Abin da ya fi yanzu mu shiga rokon Allah ni da kai, ko Allah ya amshi rokommu, ka sami haihuwa.” Nakowa ya amshi shawara da hannu bibbiyu. Suka shiga rokon Allah.


Ba su yi wata uku ba, sai Allah ya amshi rokonsu, daya daga cikin matan Nakowa ta sami ciki. Da ganin haka fa Nakowa murna ba sai an fada ba. Nakowa ya kira malamin nan ya yi masa kyauta mai yawa. Sa‘an nan ya ce da shi, "lna so mu roki Allah, matar nan tawa ta haifi da namiji, kuma Allah ya sauke ta lafiya.” Malami ya amsa, sa‘an nan ya ce, “To, bisa magana da ka fada mani, kan wai ina yi maka habaici ne, don ba ka taba haihuwa ba, da zai zama habaicin ne, to da ko kowa ya nemi irin wannan habaici, wanda karshensa ya zama alheri sabo da haka na hore ka da ka yi aiki da karshen al‘amari kada ka dubi farkon shi, don akasari farkon al‘amari ya kan zama mai kyau, amma karshensa mummuna, shi ya sa ko mutum zai rika tunawa da lahira, don ko karshe can ne makomarsa.” Malami ya yi godiya ya koma gidansa.


Da Nakowa da malami suka shiga rokon Allah, kan Allah ya sauki matar lafiya, ya kuma nufa ta haifi da namiji. A wani dare Nakowa na cikin roko sai ya ga dakin da ya ke ciki ya yi duhu, sa’an nan ya yi haske, ya duba haka gabansa sai ya ga wata irin halitta, kafafun kamar tsinke jikin kamar runbu hakoran ko kamar kwabren itace, kan ko kamar na biri. Nakowa ya ga lalle wannan halitta aljani ne ga shi ba shi mafita, sabo da haka zuciyarsa ta dake, ko da ya ke da ma jarumi ne, ya ce, “Kai, me ya kawo ka dakina ?" Aljani ya bugi kirji da hannu ya zunguri Nakowa da hakori daya, ya ce, “Ni za ka nuna wa raini?" Nakowa ya warto takobinsa ya dankara wa Aljiani har ya rabe biyu, amma da ya ke aljani ne, ya sake gamewa, ya dubi Nakowa ya haure shi da hakori, ya fadi har ya suma. Da ya farfado ya sake fada aljani suka yi ta dauki ba dadi har asuba. Da aljani ya ga Nakowa lalle ya isa duk inda jarumi ya kai ya kai, sai ya nemi su yi abota, suka yi abota. Aljani ya kawo wani takobi mai wani irin rubutu a jikinsa da larabci, ya ce, “Ka ga wannan in kana tare da shi, ko da Sarkin Aljannu ku yi fada, don ba irinsa duk duniya." Ya kuma yi masa alkawari ko wane mako zai zo su yi hira, daga nan sai ya bace. Ko wane mako yana zuwa.


Bayan wata tara matar Nakowa ta haihu, Allah bai amsa rokonsu ba ta haifi mace, wadda domin kyawo sai ka ce aljana. Ko da ya ke Nakowa bai samu cikakkiyar biyan bukata ba, amma shagalin da aka yi ran da ta haihu sai wanda ya gani. Aka yi sa’a kuwa ran nan aljani abokin Nakowa ranar zuwansa ce. Da aljani ya zo Nakowa ya ba shi labarin abin farin cikin da ya same shi. Aljani ya taya shi murna, ya yi alkawali zai zo suna tare da abokansa.


Da mako ya kewayo aka rada wa yarinya suna Zulkaratu. Nakowa ya sa aka yanka rago dari, rakuma arba'in, shanu hamsin, sha'anin abinci ko idan an tsaya a fada sai a cika littafi, a takaice dai duk garuruwa na kusa da Langeri sai da suka kwana bakwai ba su sai abinci ba. Tun daga safiyar suna a ke kade-kade da bushe-bushe, har wata safiyar.


Yawaitar wannan shagali har abin ya kai ga Limamin garin, sai Liman ya aiko wa Nakowa a fada masa wannan bidi'a ta yi yawa, ya kamata a bari haka nan, im ba kuma an fita daga hanyar Allah ba ne. Nakowa ya aika aka sanad da Liman zai yi bakin kokarinsa ya hana mutane, amma kuma Liman ya san wanda ya yi nisa ba ya jin kira, wannan mutane kafin a jawo hankalinsu su bar kada-kade da sauran sha’ani sai an yi da gaske. Nakowa ya aika wa jama’a a tashi daga biki haka nan, amma ina, ba wanda ma ya saurari abin da a ke fada.


Abin sha'awa da la'asar sai kurum aka ji kade-kade da bushe bushe da waka daga sama ana kuma watso kudi da goro, ashe aljani abokin Nakowa ne ya zo taya shi biki, kamar yadda ya dauki alkawari. Wannan fa shi ya jawo tsofaffi da dattawa ana kokawa don kudi. Maganar kudi nan da nan ta bazu gari.


Kafin a ce haka dattawa sun fi yawa gun bikin sai kokawa a ke da su.


Magana ta tafi har fada, da Liman ya ji haka, sai ya ce da Sarki, “Ashe da gangan na zargi Nakowa, ashe abin na Allah ne, kudi daga sama ai lalle baiwa ce daga Allah." Sai Liman ya ce wa Sarki, “Ai ya kamata mu tafi mu sami abin da muka samu, don neman albarka.” Kafin a ce haka sai gun biki ya cika da sarakin gari da mahukunta. Da zuwansu ba wanda ya dube su ma, kowa yana ta kansa, ganin haka fa sai Liman ya ce; “Ai ba tsayawa za mu yi ba, gara mu shiga mu ga abin da za mu samu.” Kafin a ce haka sai ga Sarki da Liman da sauran manyan gari suna kokawa da yara, an ture masu rawani can rigunan an yi kaca-kaca da su.
...Za mu ci gaba ranar Asabar da karfe tara na dare (9:00 pm), insha Allah.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user