Sunday 30 June 2019

KARANTA SANARWA DA SHAWARA GA MASU SHA'AWAR SHIGA AIKIN DAN SANDA

Tura Wannan Zuwa Ga
Idan Allah Ya kaimu jibi Litinin 1-7-2019 rundinar 'yan sandan Nigeria zata fara tantance matasa da suka cike form na neman shiga aikin 'dan sanda a duk fadin jihohin tarayyar Nigeria.Shawara mai muhimmanciMarubuci: Datti Assalafy


Shawaran da zai baiwa matasan a takaice shine:


A gurin tantancewa zaku tarar da wasu gurbatattun mutane 'yan damfara daga cikin ma'aikata ko wadanda ba ma'aikata ba, zasu ce ku bada kudi kaza zasu sama muku aiki, ina baku shawara kada ku amince da hakan


Tun daga lokacin da Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zama shugaban Kasar Nigeria aka samu canji a gurin daukar sabbin 'yan sanda, duk wata hanya na ha'inci da akebi a samu aikin ya toshe, don haka kar wani ya yadda cewa akwai wanda zai sama masa aikin ta barauniyar hanya, tsakani da Allah babu yanzu

Shawara mai Muhimmanci
Bayan haka ina tausayawa masu shan giya. taba da kwayoyi, don a gaskiya yana daga cikin tsarin da aka gabatar a gurin tantancewa, da zaran sunga alamar kana shan taba ko giya ko kwaya ba zasu tantanceka ba, saboda anaso a tsarkake aikin a samu gyara mai ma'ana


Allah Ya bawa mai rabo sa'a Amin.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user